logo

HAUSA

Masana: Sin ta samar da himma ga aikin tinkarar sauye-sauyen yanayi a fadin duniya

2020-12-16 13:58:16 CRI

A gun taron kolin sauyin yanayi da ya gudana a kwanan baya, kasar Sin ta sanar da wasu sabbin matakai hudu da za ta dauka a kokarin kara ba da gundummawarta wajen tinkarar sauyin yanayi. Masana suna ganin cewa, kasar Sin ta samar da babbar himma wajen tinkarar sauye-sauyen yanayi a fadin duniya. 

A gun taron kolin sauyin yanayi da ya gudana a ranar 12 ga wata, kasar Sin ta sanar da wasu sabbin matakai hudu da za ta dauka a kokarin kara ba da gundummawarta wajen tinkarar sauyin yanayi, matakan da suka hada da rage yawan hayaki na Carbon Dioxide da ake fitarwa kan kowane ma’aunin GDP da sama da kaso 65% bisa na shekarar 2005, sa’an nan, za a kara yawan makamashin da ake amfani da su wadanda ba su shafi man fetur da kwal da iskar gas ba zuwa kimanin kaso 25% bisa gaba dayan yawan makamashin da ake amfani da su wadanda ba su iya sabuntawa. Baya ga haka, za a kuma habaka fadin dazuzzuka da kimanin cubic mita biliyan shida bisa na shekarar 2005, tare kuma da kara samar da wutar lantarki da na’urorin samar da wuta da karfin iska da na rana zuwa kimanin kilowatts biliyan 1.2.  Matakan da kuma suka kasance sababbi tun bayan manufar da kasar ta Sin ta sanar tun bayan babbar muhawarar taron MDD karo na 75 a watan Satumba.

A ranar 14 ga watan, mataimakin shugaban kwalejin nazarin dabarun kimiyya da fasaha karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa,“A hakika, batun sauyin yanayi batu ne da ya shafi ci gaban kasa, wanda kuma ya tabbatar da makomar bunkasuwar kasar Sin, wato alkiblar kasar wajen samun ingantaccen ci gaba.”

Har wa yau, mataimakin shugaban kwamitin kwararrun nazarin sauyin yanayi na kasar Sin, Mr. He Jiankun ya bayyana cewa, ya zama dole al’ummar kasar baki daya su cimma daidaito kafin daga bisani su dauki hakikanin matakai na tabbatar da cimma burin da suka sanya gaba. Ya ce,“Na farko, ya kamata a sa kaimin gyare-gyaren tsarin sana’o’i tare da kafa tsarin sana’o’i na bola jari ba tare da gurbata muhalli ba, kuma a yi kokarin bunkasa tattalin arziki na zamani da kuma sana’o’i na amfani da kimiyyar zamani, a takaita

bunkasuwar masana’antun da suke samar da karafa da sumunti da man fetur da sauransu wadanda ke yawan amfani da makamashi, don rage yawan makamashin da ake amfani. A sa’i daya kuma, ya kamata a yi kokarin bunkasa sabbin makamashi da kuma makamashin da ake iya sabuntawa, a rage kaso makamashin da ke iya fitar da iskar Carbon, wanda zai zama sabon ginshiki na samar da karuwar tattalin arziki da guraben aikin yi a nan gaba.”

Daga nasa bangaren, shugaban cibiyar nazarin dabarun tinkarar sauyin yanayi ta kasar Sin, Mr. Xu Huaqing yana ganin cewa, kamata ya yi a kaddamar da juyin juya hali a fannonin ra’ayoyin jama’a da makamashi da kuma harkokin sayayya, a kokarin yayata salon rayuwa na kiyaye muhalli da rage fitar da hayaki da Carbon Dioxide. Yana mai cewa,“Ya zama dole al’ummarmu baki daya su bi alkiblar kasar wajen nacewa ga bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba.”

Mr. Zhao Yingmin, mataimakin ministan muhalli na kasar Sin ya kuma jaddada cewa, sabbin matakan da kasar Sin ta sanar za su iya kara samar da himma ga aikin tinkarar sauyin yanayi a fadin duniya, ya ce,“Sin babbar kasa ce da ke daukar alhakin da ke bisa wuyanta, a yayin da muke neman cimma makomar bai daya ga dukkanin al’umma, dole ne mu samar da dabarunmu da kuma gudummawarta. Sabbin matakan da aka sanar za su taimaka ga aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, don sa kaimin farfadowar tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba bayan da annobar Covid-19 ta kare. Baya ga haka, sun kuma kasance sakon da kasar Sin ta isar ga duk duniya na bin tafarkin samun ci gabanta ba tare da gurbata muhalli ba.” (Lubabatu Lei)