logo

HAUSA

Jerin ’Yan JKS Da Amurka Ta Fidda Babbar Karyar Ce Don Bata Sunan Kasar Sin

2020-12-16 16:07:53 CRI

Jerin ’Yan JKS Da Amurka Ta Fidda Babbar Karyar Ce Don Bata Sunan Kasar Sin

Kwanan baya, kafofin watsa labaran wasu kasashen yammacin duniya kamar Burtaniya da Australia da sauransu, sun ce, wani bayanin dake kunshe da sunayen wasu ‘yan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato JKS guda miliyan 1.95 na nuna cewa, ‘yan JKS suna aikin leken asiri a wasu hukumomi da kamfanonin yammacin kasashen duniya dake kasar Sin. A sa’i daya kuma, sun ce, ba su da shaidun dake gaskata wannan zargin da suka yi.

To, idan basu da shaidu, me ya sa, suka yar da da irin wannan labari game da kasar Sin?

Ko shakka babu, suna neman bata sunan kasar Sin ne kawai, domin nuna kiyayya.

Idan muka duba asalin wannan labari, za a gane gaskiyar hakan.

Da farko, kafofin watsa labaran kasashen sun ce sun sami bayani daga kungiyar hadin gwiwar nazarin manufofi kan kasar Sin wato IPAC, wadda aka kafa a watan Yuni na bana, bisa jagorancin dan majalisar dokokin kasar Amurka Marco Rubio. Gaba daya akwai mambobi guda 18 da suka zo daga kasashe 8 cikin wannan kungiya, wadanda su kan yada jita-jita game da harkokin kasar Sin dake shafar yankin Hong Kong, da jihar Xinjiang da kuma jihar Tibet da sauransu.

Kana, kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta kakaba wa Marco Rubio takunkumin, bisa yadda yake tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Shi ya sa, ya fitar da wannan jerin ‘yan JKS domin mayar da martani, wanda hakan ya kasance wata karya da ya tsara domin bata ran al’ummomin Sin.

Sa’an nan kuma, idan mun duba bayanin da kungiyar ta fidda, cewar, sabo da akwai ‘yan JKS dake aiki cikin wadannan kamfanoni da hukumomin kasashen ketare dake kasar Sin, shi ya sa, ake ganin cewa, kasar Sin tana leken asirin kasashen. Lalle sun yi wannan zato ne domin rashin sani game da kasar Sin, ko kuma kawai, suna neman bata sunan kasar ta Sin ne bisa wannan hujja maras tushe.

A hakika dai, gaba daya akwai ‘yan JKS kimanin miliyan 92 a kasar Sin, wadanda suke aiki a sana’oi iri daban daban, shi ya sa, ba abin mamaki ba ne, ace akwai ‘yan JKS dake aiki cikin hukumomi ko kamfanonin ketare dake kasar Sin. Suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, sun kuma samu amincewa daga kamfanoninsu. Haka kuma, wadannan kafofin yada labaran yammacin duniya sun ce, a halin yanzu, babu shaidun dake nuna cewa, akwai ‘yan JKS dake gudanar da aikin leken asiri. Lalle ba su da hankali.

Bisa wadannan dalilai, gaskiyar lamarin shi ne, wannan babbar karya ce da masu adawa da kasar Sin na yammacin kasashen duniya suka tsara, domin bata sunan kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)