logo

HAUSA

Matasa Tushen Ci Gaban Kasa

2020-12-16 17:11:26 CRI

Matasa Tushen Ci Gaban Kasa

Yayin da al’ummar duniya ke kukan irin barnar da annobar COVID-19 ke ci gaba da yiwa wasu sassa na duniya, sai ga shi asusun kula da kananan yara na MDD UNCEF ya wallafa wani rahoton hadin gwiwa da kungiyar sadarwa ta duniya cewa, kaso 2 bisa 3 na yara ’yan makaranta ko yara biliyan 3 dake tsakanin shekaru 3 zuwa 17, ba su da layin sadarwar intanet a gidajensu.

Rahoton mai taken “Yara da matasa nawa ne suke da layin sadarwar intanet a gida?” Ya kuma ce haka batun yake tsakanin matasa ’yan shekaru 15 zuwa 24 wato kimanin miliyan 759 ko kaso 63 na matasa ba su da layin sadarwar intanet a gidajensu. A matsayinsu na kashin bayan ci gaban kowace al’umma, wannan ba karamin tasiri zai yi ga ci gaban kasa ba.

Masana na cewa, yadda yara da matasa da dama ba su da layin sadarwar intanet, ya zarce batun gibi a fannin sadarwar zamani, domin rashin layin sadarwa ta intanet, zai hana su damar shiga yanar gizo da ma yin gogayya a fannin tattalin arzikin zamani da sauran fannoni na rayuwa, matakin da ka iya nisanta su da duk wani irin ci gaba da duniya ta samu a fannin ci gaban zamani.

Haka kuma, yayin da aka rufe makarantu sakamakon annobar COVID-19 wadda ke ci gaba da addabar wasu sassa na duniya, lamarin na sanya su asarar karatu. Kana rashin layin sadarwar intanet zai yi lahani ga makomar zuri’a ta gaba.

A takaice binciken ya kara bankado cewa, akwai gibi ta fuskar wurare a kasashe da ma yankuna. Wato kusan kaso 60 na yara ’yan makaranta a duniya dake rayuwa a birane ba su da layin sadarwar intanet a gidajensu, idan aka kwatanta da kusan 3 bisa 4 na takwarorinsu dake zaune a yankunan karkara.

Wannan matsalar dai kusan ta fi shafar yaran dake yankin kudu da hamadar Sahara da na kudancin Asiya, inda ake samun yara 9 daga cikin 10 ba su da layin sadarwar intanet. Idan har ana fatan samun manyan gobe da za su ci gajiyar sabbin fasahohin zamani har ma su iya bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban kasashensu, to wajibi ne gwamnatoci da wadanda alhakin hakan ya rataya a wuyansu da su samar da wadannan kayayyaki ba tare da nuna bambanci ba. Su kuma yaran da aka samar musu wadannan fasahohi na zamani, su yi kyakkyawan amfani da su ta hanyar da ta dace. Yara fa su ne manyan Gobe. (Ibrahim Yaya)