logo

HAUSA

Wang Zhenhai da sha’aninsa na yawon shakatawa a gidajen manoma

2020-12-15 15:10:53 CRI

Wang Zhenhai da sha’aninsa na yawon shakatawa a gidajen manoma

Karkashin manufofi da matakan gwamnati, mazauna jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, na kyautata rayuwarsu ta hanyar gudanar da sana’o’i daban-daban. Misali, Wang Zhenhai mai shekaru 48, na cike da farin ciki da gamsuwa da zaman rayuwarsa a yau. Wang da iyalansa suka kunshi mutane 4, na zaune ne a kyauyen Huangquxia dake garin Jiujianlou na birnin Wusu dake yankin Tacheng na jihar Xinjiang. Babban dansa na aiki a birnin Karamay, yayin da karamin kuma ke karatu a makarantar midil. Shi da matarsa, suna zama a cikin gidansu mai dakuna 3 masu fadi da haske, hakan ya sa, Wang ya fara gudanar da aikin bada hidima ga masu yawon shakatawa.

 “Na bude dakin cin abinci. Zuwa yanzu, shekaru hudu kenan ina wannan aiki. Shekara ta farko na sayar da kaji dari 4 ko 5, ta biyu kuwa na sayar da dari 7 ko 8, ta uku kuma, adadin ya kai fiye da dubu.”

Matar Wang Zhenhai ta kware wajen dafa abinci, har abokai da makwata suna yabawa mata matuka. Shekaru 4 da suka gabata, Wang da matarsa sun fara aikin bada hidima ga masu yawon shakatawa, karkashin goyon bayan gwamnatin kyauyensu, abincinsu mafi shahara shi ne “Naman kaza da aka yanka kashi 8”. Sun kirkiro wannan abinci ne bisa shahararren aibncin nan mai suna “Dapanji” wato soyayyar kaza da dankali. Wannan abinci akwai dadi matuka, domin ya samu karbuwa daga masu yawon shakatawa.

 “Wannan abincin nawa ya yi suna sosai a yankin Wusu da Kuitun da kuma Dushanzi. Yawan kajin da Wang ke sayarwa a ko wace shekara ya kai fiye da 1500, wato 6 ko 7 a ko wace rana.”

Wata mambar kwamitin jam’iyyar JKS na garin Jiujianlou Jia Rongxia tana alfahari da wannan abinci, ta ce:

 “Masu yawon shakatawa na yabawa wannan abinci sosai, har suna sake ziyartar wurin. Ba shakka, yawan kudin shigar iyalan Wang Zhenhai ya kai kudin Sin Yuan fiye da dubu 200 a ko wace shekara.”

Wang Zhenhai ya yi bayani kan wannan abinci, yana cewa:

 “Mutane kan zo yau da kullum, wasu suna fitar da abincin daga nan zuwa yankin Kuitun da Wusu. Hakan ya sa, akwai bukatar yin oda kafin lokaci. A lokacin yanayin zafi, mutane da dama suna zuwa nan don dandana abincin, har dakin yana cika da mutane. Wasu kan kwashe rabin awa ko awa daya suna jira a kofa ko a cikin mota. Wasu mutane sun zo don fitar da abinci zuwa waje, a jiya ma akwai wasu da suka zo daga birnin Urumqi”.

Mutanen daga birnin Urumqi sun kwashe awo’i 3 ko fiye suna tuka mota zuwa wurin Wang Zhenhai don dandana wannan abinci. Saboda akwai dadi matuka ga kuma rahusa.

Wang ya ce, a lokacin da ba shi da isassun kaji, sai ya saya daga makwabta, abun da ke sa su yi farin ciki sosai.

Ban da sayen kaji daga sauran mutane, Wang ya kan sayi masara daga wajen sauran mazauna don ciyar da kaji.

Manoma suna farin ciki matuka saboda samun karin kudin shiga. Garin JiuJianlou ya fitar da manufofi ko matakan tallafawa manoma da dama, alal misali a kyauen Huangquxia da Wang Zhenhai ke zama, an gabatar da ajin horo a lokacin hunturu. Matar Wang Zhenhai ta kan shiga ajin. Ta ce:

 “Na koyi ilmin dafa abinci. Kwararren Malami na koyar da ni abinci iri daban-daban. Ban da wannan kuma, an koyar da mu fasahar kiwon kaji.”

Sha’anin Wang Zhenhai na bunkasa matuka karkashin taimakon gwamnati da kuma kokarinsu. Abin da ya sa zaman rayuwar iyalan Wang Zhenhai ke kyautatuwa matuka. Yanzu, Wang ya zama abin misali ga sauran manoma. Game da makomarsu, Wang na da shiri mai kyau, yana fatan bude sassan dakin cin abincinsa a sauran wurare. Ya ce:

 “Shugaba Xi Jinping ya ce, kamata ya yi mu yi iyakacin kokari don samun zaman rayuwa mai kyau, na amince da shi kuma ina kokarin neman zaman rayuwa mai armashi.”(Amina Xu)