logo

HAUSA

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

2020-12-15 14:47:23 CRI

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

Kasar Sin da kasashen Afirka suna inganta hadin-gwiwa da mu’amala a fannoni da dama a halin yanzu, musamman a karkashin tsarin FOCAC wato tsarin dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka, gami da shawarar “ziri daya da hanya daya” da shugaba Xi Jinping ya bayar.

Idan mun dauki tarayyar Najeriya a matsayin misali, akwai muhimman ababen more rayuwar al’umma da dama, wadanda suka shaida irin hadin-gwiwa da mu’amalar da aka yi tsakanin ta da kamfanonin kasar Sin, ciki har da sabuwar tashar jiragen sama da aka gina a filin saukar jiragen sama na Namdi Azikiwe dake Abuja, da tashar jiragen ruwa dake Lekki, da layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, da sauransu. Dukkan wadannan ayyukan hadin-gwiwar suna taimakawa sosai, ga inganta rayuwar jama’ar wurin, har ma da raya tattalin arziki, da samar da dimbin guraban ayyukan yi.

Abun lura a nan shi ne, ban da ababen more rayuwar al’umma da kamfanonin kasar Sin suka inganta a Najeriya, da ma sauran kasashen Afirka, akwai fannin da ya shafi aikin gona, wanda kamfanonin kasar Sin suke bada taimakon rayawa a Najeriya. Kamfanin Yuan’s Seed na daya daga cikinsu.

An kafa kamfanin Yuan’s Seed mai kula da harkokin nomawa, gami da cinikin shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya a shekara ta 2010. A halin yanzu kamfanin na gudanar da ayyukan noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya, ko kuma “hybrid rice” a turance a wasu kasashen Asiya da Afirka da dama, ciki har da Pakistan, da Bangladesh, da Vietnam, da Philippines, da Indonesiya da Madagascar. Kamfanin ya fara noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya a Afirka a shekara ta 2008, wato a kasar Madagascar ke nan, har kwalliya ta biya kudin sabulu. Sa’annan a shekara ta 2016, kamfanin Yuan’s Seed ya daddale yarjejeniyar hadin-gwiwa da shahararren kamfanin kasar Sin dake Najeriya mai suna Lee Group, domin fara aiki a kasar.

Madam Wan Jueming ita ce sakatariyar kwamitin shugabannin kamfanin Yuan’s Seed, wadda ta bayyana cewa:

“A watan Yulin shekara ta 2016, kamfaninmu ya tura wasu kwararru zuwa Najeriya, don fara aikin gwajin noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya a wasu yankuna biyu dake arewacin Najeriya, ciki har da Kano da Jigawa, kuma dukkansu sun samu nasara. Wato matsakaicin yawan shinkafar da muka samu ya kai ton 7.5 a kowace hekta, kuma mafi yawa ya kai ton 9.8 a kowace hekta. Har yau, ingancin shinkafar da muka yi gwajin nomawa ya dace da bukatun mazauna wurin. Saboda haka, a shekara ta 2019, kamfaninmu da kamfanin Lee Group, sun kafa wani kamfani na hadaka domin noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya ta kasar Sin.”

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

Madam Wan ta kara da cewa, daga shekara ta 2016 zuwa 2019, kamfanin Yuan’s Seed ya hada kai da kamfanin Lee Group don gwaje-gwajen noman wasu nau’o’in shinkafar da yawansu ya kai 23. A karshe an zabo nau’o’i 3 daga cikinsu, wadanda za’a tallata nomansu a arewacin Najeriya.

Yi Baoshu na daya daga cikin kwararrun jami’an aikin noma da kamfanin Yuan’s Seed ya tura zuwa Najeriya, wanda ya yi shekara daya yana gwajin noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya ta kasar Sin a shekara ta 2019. Ya bayyana sirrin nasarar da suka samu, inda ya ce:

“Bisa gwajin da na yi a Najeriya, a hakikanin gaskiya, noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya ya dace sosai da halin da ake ciki a Najeriya. A bara, na yi gwajin noman shinkafar a hekta daya a Jigawa, kuma yawan shinkafar da muka girba ya kai ton 8.3. Sirrin shinkafarmu shi ne, za’a iya yin girbi mai tarin yawa, kuma mai maganin cututtuka da kwari. A lokacin girbin, manoman dake zaune a kusa da wurin, sun zo ganin yadda muke iya girbin shinkafar mai yawan gaske, inda suka jinjina da cewa NO. 1! NO. 1!”

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

Arewacin Najeriya na da dogon tarihi na gudanar da aikin noma, kuma manoman wurin suna da kwarewa sosai wajen noman shinkafa da sauran wasu amfanin gona. Amma zuwan kamfanin Yuan’s Seed na kasar Sin yana kawo musu wasu sabbin hanyoyi, da fasahohi, gami da na’urorin aikin gona, wadanda ba’a taba ganinsu ba a da.

Manajan kula da aikin Najeriya na kamfanin Yuan’s Seed Wang Jian, ya bayyana cewa farkon zuwansu arewacin kasar, manoman wurin sun nuna shakku game da aikin gwajin da suka yi, inda ya ce:

“Na farko, ba su taba ganin fasaharmu ta fesa irin shinkafa kai-tsaye a gona ba. Suna shakkun cewa, idan mun fesa irin a nan, ko za’a shanya shi ne har ya bushe? Na biyu, noman shinkafarmu wato shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya ba ya bukatar matakai masu yawa, wato babu bukatar idan shinkafa ta fito, mu cire shi mu sake dasa shi a wani wuri na daban, ba bukatar canza wurin. Manoman wurin su ma sun nuna shakku kan wannan fasaha.”

Mista Wang ya ce, duk da shakkun da suka nuna, manoman wurin sun nuna matukar sha’awa game da fasahohin kasar Sin na noman wannan sabon nau’in shinkafa. Shi ya sa a bara, kamfanin Yuan’s Seed ya kebe wani wuri mai fadin murabba’in mita 1000 ga wani manomin wurin dake Jigawa, aka ba shi ire-iren shinkafar kasar Sin. Daga baya ya kwaikwayi fasahar kasar Sin ta fesa maganin kashe kwari, da amfani da takin zamaninsu, har a karshe ya yi girbin shinkafar da matsakaicin yawanta ya zarce ton 6 a kowace hekta, wanda ya ninka abun da yake girbewa a baya. Wannan abu ya karfafa gwiwar manoman wurin sosai, har akwai wasunsu wadanda suka fara aiki a kamfanin Yuan’s Seed dake jihar Jigawa.

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

Malam Saleh Adamu, wani manomi ne kana dan kasuwa ne, wanda ya taba yiwa kamfanin aiki na wasu watanni. Ya ce, fasahar kasar Sin ta noman shinkafa tana matukar burge shi, mutanen China ma sun koya masa fasahar noma ta zamani, inda ya ce:

“Injiniyan shinkafa na kasar Sin gaskiya yana da kwarewa akan aiki sosai, domin ya kara mana ilmummuka akan noman shinkafa, yanda ake yinsa a China. Domin lokacin da muke aiki tare da shi, mun samu basira da yawa a kan shinkafa, wanda ba mu sani ba da, mun koyi gyaran kasa da yadda suke gyaggyarawa, wajen ita kanta shinkafar yanda ake ba ta ruwa da yanda ake fitar mata ruwa, duk mun ga abubuwan da suka yi na fasaha, to amma wannan iri da aka raina, hekta daya muka yi kawai. Watanmu 3 da su. Mun gama aiki da su, mun ji dadin komai da komai. Sun koma gida. Bayan da suka koma gida kuma za su dawo, za mu ci gaba da aiki, za mu yi kamar hekta ta kai dari za mu yi da su, sai wannan Corona ta fito. Akwai Abdullahi, shi ne ke musu tafinta domin a lokacin ba sa jin Hausa, amma duk da haka mun zauna da su lafiya, domin suna mana zance da hannu, mu ma muna musu zance da hannu. Haka muka yi rayuwa muna yin aiki.

Gaskiya mun ga amfanin irin sosai, sakamakon irin da muke amfani da shi, muna samun buhu talatin a eka daya, su nasu muna iya samun buhu 40 ko 45. Domin akwai wanda ya yi eka daya da irin da muka gwada, sai da aka samu buhu 48. Da aka yi hekta daya kuwa sai da aka samu buhu dari da goma sha shida.”

Malam Saleh Adamu ya ce, akwai babban bambanci tsakanin aikin noman shinkafa na Najeriya da na kasar Sin, inda ya ce:

“Akwai bambanci 100%. Akwai wani aiki da muke yi na gargajiya da muke kife kasa sai mu shuka shinkafa, amma su sai suka zo da motar da take juya kasar, ko ba taki aka shuka shinkafa a wurin fitowa za ta yi, bare kuma aka sa taki. Kuma takinsu dan waje ne, namu bai kai nasu karfi ba. Kuma gaskiyar magana, aikinsu akwai bambanci da namu sosai.”

Najeriya, kasa ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, wadda take shigowa da shinkafa daga ketare da yawansu ya kai ton miliyan 2.8 zuwa miliyan 3 a kowace shekara. Kuma yawan kudin da gwamnatin kasar ta kan kashe a fannin ya kai kimanin dala biliyan 2.3. Saboda haka, gwamnatin tarayya ta tsara wasu manufofin gatanci don tallafawa manoman kasar, ciki har da ba su kudin rangwame don sayen iri, da takin zamani da injunan aikin gona, a wani kokari na karfafa musu gwiwar shuka shinkafa da kansu. Hakan ya baiwa kamfanin Yuan’s Seed na kasar Sin damar bunkasa harkokinsu na noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya.

Manajan kula da aikin Najeriya na kamfanin Yuan’s Seed Wang Jian ya yi karin haske kan ma’anar noman shinkafar kasar Sin a Najeriya, inda ya ce:

“Idan mun iya gudanar da aikinmu yadda ya kamata a Najeriya, wato noman shinkafar kasar Sin a gonaki da fadinsu ya kai hekta dubu 20 a wasu sassa hudu dake Najeriya, za mu samu girbin shinkafar da yawansu ya kai ton dubu 140 a kowane yanayin noma, abun da zai baiwa mutane dubu 720 shinkafa. Hakan zai taimaka sosai ga warware matsalar rashin abinci a wurin. Har wa yau, za mu iya samar da dimbin guraban ayyukan yi ga mazauna wurin, kuma a kowane yanayin noma, za mu dauki hayar ma’aikata 8000.”

Kamfanin kasar Sin yana taimakawa Najeriya bunkasa aikin noman shinkafa

Shi ma malam Saleh Adamu ya bayyana kyakkyawan fatansa ga karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya a fannin noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya, inda ya ce:

“Gaskiya idan shugabanninmu za su bada hadin kai ga kasar Sin, za a samu ci gaba sosai da sosai. Da shugabanni za su bada hadin kai da mun wuce wannan wurin, sai dai su dora mu akan wani abu kuma. Zuwansu hekta daya muka yi kadai, amma na karu da aikin gona sosai na ga amfanin zama da su. Rayuwata ta canza, don sun kara karantar da ni abun da na amfana. Domin shinkafar da na noma bayan mun rabu da su, na kamanta irin fasahar da suka zo da ita, to amma ba ni da na’urori irin nasu.”

Shi ma a nasa bangaren, Liu Guoxiang, mataimakin babban manajan kamfanin Yuan’s Seed ya bayyana fatansa cewa:

“Idan mun tabo magana kan ayyukan hadin-gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka, mutanen Afirka sun amince da hanyoyin mota da gadoji, da sauran wasu muhimman ababen more rayuwar jama’a da muka gina musu. Amma idan mun tabo magana kan hadin-gwiwar aikin noma, mutanen Afirka suna ganin cewa, idan kwararrun China sun bar wajen, aikin zai tsaya nan da nan, ba zai dore ba. Shi ya sa abun da muke fata shi ne, mu lalibo wata sabuwar hanya, mu shiga cikin kananan hukumomi dake Najeriya, ba wai mu je can mu noma wani abu mu yi girbi mu nuna musu kawai mu tafi ba, gaskiya muna son yin wani abu a can.”

Malam bahaushe kan ce, noma tushen arziki. Ana fatan kara inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya a fannin noman shinkafar da aka inganta irinta ta hanyar kimiyya, domin kowane bangare ya ci alfanu. (Murtala Zhang)