logo

HAUSA

Deng Lu, Sarauniya mai daura na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam

2020-12-14 21:57:44 CRI

Na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam na’ura ce da ake amfani da ita wajen daidaita zaman kyamara, wadda ke iya daukar hoto yadda ya kamata ko da ana motsi. Na’urar Steadicam ta yi kama da wani nau’in riga, wadda take bukatar a sanya ta a jiki yayin da ake amfani da ita. Saboda baki dayan kayayyakin dake jikin na’urar kamar kyamar da batir da fuskar kyamarar dake nuna hoto, suna da nauyi, wani lokaci su kan kai nauyin kilogiram 30, rigar na baje nauyin yadda ya kamata sosai.

Motsawa bangarori da dama yayin da ake sanye da wannan na’ura mai nauyi ba abu ne mai sauki ba, kuma zai iya rinjayar mutum, musammam a lokacin daukar bidiyo mai tsawo. La’akari da yadda aikin tafiyar da na’urar yake, amfani da ita aiki ne da maza suka mamaye.

Deng Lu, Sarauniya mai daura na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam

A wasu kasashen, akwai kwasa-kwasai na musammam da ake yi domin taimakawa mutane amfani da na’urar yadda ya kamata. Bayan an kammala kwas, sai a samu takardar shaidar kwarewa. Sai dai, galibin mutane a kasar Sin ba su da ilimin amfani da na’urar, mutane kalilan ne suka samu horon da ake bukata. Deng Lu ta kuduri niyyar shawo kan dukkan wani cikas da za ta gamu da shi, kuma ta jure wahalhalu da dama da suka tsallake tunanin mutane bare su fahimta. Sai da ta shafe shekaru 10 kafin ta kai matakin kwarewar amfani da na’urar.

A shekarar 2015, Deng ta zama mace ta farko a kasar Sin da ta dauki bidiyon gasar kungiyoyin kwallon kafa ta kasar Sin. Sai kuma a watan Mayun 2020, wani bidiyo mai tsawon dakiku 74 na yadda take aiki ya fara yawo a shafin Intanet.

A cikin bidiyon, an ga yadda take da sauri da zafin nama, ko a lokaci mai sarkakiya, al’amarin da ya sanya tunani a zukatan masu amfani da Intanet. A sa’an nan ne kuma suka fara kiranta da “Sarauniya mai daura na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam”.

Deng Lu ta ce:“Har yanzu da saura. Ina son zama daraktar mai daukar hoton wadda za ta iya daukar bidiyo masu inganci.”  

An haifi Deng Lu ne a Beijing, kuma iyayenta sun kasance ma’aikata a masana’antar shirya fina-finai. Babanta da kakanta masu daukar hoto ne, yayin da mahaifiyarta da kakarta suka kasance masu tsara tufafi. A lokacin da take yarinya, ta ga yadda ayyukan masana’antar suke. Sai dai burin mahaifinta shi ne, ta yi aikin ofis mai kyau, amma ba a masana’atar shirya fina-finai ba.

Da farko, ta samu aiki a wata madabba’a, kamar yadda babanta ya bukata, amma ba ta jin ta gamsu da rayuwarta. Saboda sha’awar daukar bidiyo, ta bar aikin a lokacin tana da shekaru 17, inda ta shiga wata tawagar masu shirya dirama.

Shirin dirama na farko da ta shiga shi ne na Fox Volant of the Snowy Mountain na 2007, wani dirama da ya samo asali daga littafin fasahohin Kongfu na Jin Yong (Loius Cha Leung-Yung). ‘Yar wasan yankin Hong Kong Athena Chu ce ta kasance jarumar shirin. Deng Lu ta yi aiki a matsayin mataimakiyar mahaifiyarta, wadda ke tsara tufafi. Karkashin jagorancin mahaifiyarta, Deng ta koyi yadda ake tsara tufafi. Ta kuma yi aikin wucin gadi a matsayin mai taimakawa jarumi, wato mai ajiye lasfika da shirya wurare.

Deng Lu, Sarauniya mai daura na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam

Shirin Bodyguards and Assasins na 2009, na bukatar ‘yan wasa su sanya tsoffin dan kwalaye. Da hannu Deng ta dinka dan kwalayen ta kuma rina su domin su yi kama da sun tsufa. Deng ta yi matukar gamsuwa da aikinta bayan ta ga yadda yanayin dan kwalayen suka kai a cikin bidiyo.

A matsayin daya daga cikin ma’aikatan shirin The Revolution 1911 na shekarar 2011, aikin Deng Lu shi ne kula da tufafin Darakta kuma Jarumi Jackie Chan. Ta kan dauki tufafin tana bin Jackie Chan yayin da yake gudu tsakanin tsaunika a lokacin daukar shirin.

A wani lokaci, ta fadi a kan titi ta ji rauni a kafarta, har ya yi ta jini. Duk da cewa Jackie Chan ya ce ba sai ta yi gudu ba, Deng ta yi ta bin shi da tufafin. Daukar shirin fim na bukatar aiki tare kuma dole ne kowa ya bada gudummuwarsa. Wannan shi ne abun da Deng ta koya a matsayin mataimakiyar mai tsara tufafi.

A lokacin da ba ta da aiki, Deng kan yi amfani da kyamararta wajen daukar hotuna da bidiyon abubuwa masu ban sha’awa na ma’aikatan a lokacin da ake daukar shiri, sai kuma ta sake tsara su zuwa shirin Documentary. Aikin nata ya burge darakta, inda ya ba ta shawarar zama mataimakiyar mai daukar hoto. Ta kuma yanke shawarar gwadawa. A lokacin da take da shekaru 21, Deng ta kwashe dukkan kudin da take tarawa Yuan 20,000 ta saye karamar na’urar tsayayyen kyamara ta Steadicam ta farko.

Deng Lu ta taba tattaunawa da Darakta Stephen Tung Wai a lokacin da take da shekaru 21, inda ya ce mata, “idan ba ki fahimci wata dabara ta samun ci gaba, za ki sha wahalar cimma burinki, ko da kina da kuzari sosai.” Kalamansa sun karfafa mata gwiwa, inda ta fara daukar sabuwar alkibla a duniyar shirya fina-finai.

Sauya aiki ba abu ne mai sauki ba. Ta kan yi ayyuka masu karancin albashi amma kuma masu wahala. Wadannan damammaki na bai wa Deng Lu damar kara gogewa. Daga baya dai, ta nemi gurbin karo ilimi na shekara 1 a sashen nazarin daukar hoto na kwalejin nazarin shirya fina-finai ta Beijing.

Domin tabbatar da yanayin karfinta ya yi daidai da na takwarorinta maza masu daukar hoto, Deng ta fara gudu da tsalle-tsalle da daga nauyi. Ta kan motsa jiki na tsawon sa’o’i 7 zuwa 8 a ko wace rana, musammam a lokacin da take cikin shekaru 20. Ta kan yi ninkaya a lokacin da take son hutawa da samun nutsuwa. Yawancin kawayenta na kiranta da mai son motsa jiki, amma ta yi ammana ba za ta zama kwararriyar mai taimakawa daukar hoto ba idan har daukar kayayyaki bai zama abu mai sauki a wajenta ba.

Deng Lu, Sarauniya mai daura na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam

A lokacin da Deng Lu ta fara koyon amfani da na’urar tsayar da kyamara ta Steadicam, ta kusa yanke jiki ta fadi, saboda ciwon baya. Amma ba ta hakura ba. A lokacin da take daukar shirin fim din Love Education a shekarar 2017, ta yi mamakin nauyin na’urar da kyamara kirar Sony samfurin F65 dake bayanta. A lokacin ta fahimci dalilin da ya sa mata kalilan ne kadai ke gwada irin aikin.

Yayin da take daukar shirin fim, Deng kan yi aiki na tsawon a kalla sa’o’i16 a ko wace rana. A yawancin lokutan, ba ta iya sauke na’urar. Wata rana, ta dauki shiri na sama da sa’o’i 40 ba tare da tsayawa ba. Baya ga aiki na tsawon lokaci, akwai gajiya da rashin cin abinci mai kyau, a wani lokaci har da rashin yanayi mai kyau.

Deng Lu kan yi iya bakin kokarin ganin ta saba da yanayi maras kyau. Ta taba aiki a kasan babbar ganuwa da tsakar dare, haka kuma ta taba shiga hamada da tsaunika masu kankara da dazukan dake da macizai da kunamu. Jin rauni kuwa, ya zame mata jiki.

Wata rana, yayin da ake daukar shiri, kwatsam sai aka samu iska mai karfi da ta ture fitilar dake saman kan Deng. Fitilar ta buga kanta. Sai da aka kai ta asibiti. “Ba za ka taba sanin abun da za ka gamu da shi ba a wajen aiki. Babu abun da zan iya yi sai hakuri. Idan na yi niyyar yin wani abu, ina fatan kammalawa….ko da kuwa akwai wahala,” cewar Deng.

Deng Lu jajirtacciya ce. Duk yadda mutane suka nuna gazawarta, haka take jajircewa wajen ganin ta gyara aikinta. Bisa la’akari da jajircewarta da karsashi, kawayenta kan kirata da “mahaukaciya” a wasu lokuta. Deng ta taba hawa fiffiken jirgi, da na’urarta ta tsayar da kyamara, amma kuma ba tare da rigar kariya ba. Ta dauki shiri a saman tsauni mai dusar kankara da na’urar mai nauyi. Ta kuma dauki wasu bangarorin shiri a karamar mota mai matukar gudu, domin ta inganta yanayin saurin shirin.

“Yanzu da na fara, ina son yi da kyau, da nacewa a kai har karshen rayuwata,” cewar Deng Lu. Ta kara da cewa, a kalla a wajenta, duniyar fina-finai kamar Jianghu, wanda ke nufin wani abun sha’awa na fasahar Kongfu ta Sinawa, ko kuma wata duniyar tatsuniya.

Deng Lu na shirin ci gaba da aiki a matsayin darakta a fagen daukar hoto, domin kara gogewa a aikin. Idan ta samu dama, kila za ta gwada aikin bada umarni da shirin fim dinta na kanta, watakila fim mai kama da Amelie na shekarar 2001, wanda zai ba mutane damar fahimtar rayuwa.(Kande Gao)