logo

HAUSA

Ana sa ran cinikin motoci a kasar Sin zai kai miliyan 25 a wannan shekara

2020-12-14 11:44:58 CRI

Bisa bayanan da kungiyar kamfanonin hada motoci ta kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, ana sa ran cinikin motoci a kasar Sin zai iya kaiwa miliyan 25 a wannan shekara ta 2020, sama da yadda aka yi tsammani tun a farkon wannan shekarar, lamarin da ya bayyana a fili yadda kamfanonin kera motoci na kasar Sin ke samun matukar ci gaba, kuma hakan ya nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke samun bunkasuwa.

Kasar Sin tana kara hanzarta gina sabon tsarin ci gaba ta yadda dukkan bangarorin tattalin arzikinta na cikin gida da na ketare suke taka gaggarumar rawa sannan bangarorin biyu na gida da na waje suna ci gaba da tallafawa junansu. Tabbas ne bangarorin biyu za su daga matsayin bukatun kasuwannin hada motoci domin samun karin bunkasuwar fannin. Kungiyar kamfanonin hada motoci ta kasar Sin ta yi hasashen cewa kasuwar hada motocin za ta samu ja da baya a shekara mai zuwa amma za ta daidaita nan da shekaru 5 masu zuwa, inda ake sa ran cinikin motocin zai iya kaiwa miliyan 30 nan da shekarar 2025. (Ahmad)