logo

HAUSA

Tsarin zaman al’ummar Sin ya sake shaida burin kasar na mayar da moriyar al’umma gaban kome

2020-12-13 16:03:31 CRI

Tsarin zaman al’ummar Sin ya sake shaida burin kasar na mayar da moriyar al’umma gaban kome

A yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa bisa shekaru biyar biyar na 13 tsakanin shekarar 2016 zuwa shekarar 2020 a kasar Sin, ana kara kyautata tsarin tabbatar da zamantakewar al’ummar kasar, wanda ya fi girma a fadin duniya, saboda yana shafar al’umma mafi yawa, lamarin da ya sake shaida cewa, a ko da yaushe gwamnatin kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tana mayar da moriyar al’ummarta a gaban kome.

Rahotannin sun nuna cewa, tun daga shekarar 2016, gwamnatin kasar Sin ta fara gudanar da aikin yin rajista ga daukacin al’ummar kasar, wadanda yawansu ya kai miliyan 1390, domin tabbatar da shigarsu tsarin zamantakewar al’ummar kasar. Ya zuwa karshen watan Oktoban bana, yawan mutanen da suka shiga inshorar ritaya a kasar ya kai miliyan 992, wadanda suka shiga inshorar rasa aikin yi sun kai miliyan 214, kuma adadin mutanen da suka shiga inshorar jin raunuka yayin aiki ya kai miliyan 264, a bayyane an lura cewa, an kammala aikin kafin wa’adin da aka tsara.

Abun da ya fi jawo hankali shi ne, kusan daukacin al’ummar kasar ta Sin wadanda suka taba fama da kangin talauci sun shiga inshorar ritaya, har adadin ya kai kaso 99.99 bisa dari, kuma a halin da ake ciki yanzu, adadin mutanen da suka shiga inshorar ritaya a kasar Sin ya kai kashi daya bisa uku na daukacin mutanen da suka shiga inshorar ritaya a fadin duniya, wato tsarin inshorar ritaya na kasar Sin ya shafi al’umma mafi yawa a duniya.

Hakika aikin tabbatar da zamantakewar al’ummar kasar Sin ya shiga wani sabon matakin ci gaba a tarihi, alal misali adadin mutanen da suka shiga tsarin yana kara karuwa a kai a kai, ingancin tsarin yana kara kyautatuwa a bayyane, bisa ci gaban tattalin arzikin kasar.

Kana domin kyautata aikin samar da hidima ga al’umma, gwamnatin kasar ta Sin tana kara mai da hankali kan kafa tsare-tsaren hidimar jama’a da kafa dandalin samar da bayanai ga al’umma a bangaren, ta hanyar samar da katin zamani yayin da ake tabbatar da zamantakewar al’umma, ya zuwa karshen watan Nuwamban bana, adadin mutanen da suke amfani da katin a fadin kasar ya riga ya kai miliyan 314, wato suna jin dadin hidimar da ake samarwa ta hanyar yin amfani da manhajoji sama da 419.

Duk wadannan sun sake shaida cewa, gwamnatin kasar Sin tana mayar da moriyar al’ummarta a matakin farko, kamar yadda babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Xi Jinping ya bayyana, moriyar al’ummar kasarsa ta fi kome muhimmanci, ya dace a yi kokari domin cimma burin kara kyautata rayuwar al’ummar kasar, tare kuma da samar musu jin dadin rayuwa da tsaro mai dorewa. (Jamila)