logo

HAUSA

Cutar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Huldar Hadin Kan Sin Da Afirka Ba

2020-12-12 22:20:03 CRI

Cutar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Huldar Hadin Kan Sin Da Afirka Ba

“Ci gaban huldar hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba zai taba tsayawa ba. Ko cutar COVID-19 ma ba za ta hana ci gaban hadin kan Afirka da Sin ba.” Mamadou Ndiaye, shi ne jakadan kasar Senegal a kasar Sin, ya fadi haka ne yayin da yake halartar taron manyan jami’ai karon 14 a karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ya gudana a ranar 10 ga wata, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Hakika maimakon hana gudanar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, ma iya cewa cutar COVID-19 ya zama wani dalilin da ya sa ake samun karin damammakin hadin kai a tsakanin bangarorin 2, musamman ma a fannin aikin likitanci da samar da magani. A lokacin da kasar Sin ke fama da yanayin cutar COVID-19 mai tsanani, ko da wasu kasashen Afirka marasa karfin tattalin arziki irinsu Equatorial Guinea, da Djibouti ma sun ba da tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 2 da miliyan 1 ga kasar Sin.

Cutar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Huldar Hadin Kan Sin Da Afirka Ba

Daga bisani, bayan da aka samu barkewar annobar COVID-19 a nahiyar Afirka, kasar Sin ita ma ta yi kokari kai wa kasashen Afirka dauki cikin gaggawa. Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta aike da dimbin kayayyakin kandagarkin cuta zuwa ga kasashe fiye da 50 dake nahiyar Afirka, gami da kungiyar tarayyar Afirka ta AU. Kana ta tura tawagogin kwararrun aikin likitanci fiye da 10 zuwa kasashen Afirka, wadanda suka kunshi likitoci fiye da 160. Haka zalika, kasar ta kira tarukan musayar fasahohi tsakanin kwararun kasar Sin da na kasashen Afirka, don raba fasahohin da ta samu a fannin dakile cutar COVID-19 tare da kasashen Afirka.

Sinawa su kan ce, “ a lokacin da ake gamuwa da matsala, za a san wane ne aboki na gaske.” Yadda kasashen Afirka da kasar Sin suke kokarin taimakawa juna a yayin da ake fuskantar annoba, ya shaida zumunci mai zurfi da ya kasance tsakanin bangarorin 2. Sai dai ko ba a lokacin da ake fama da annoba ba, an riga an samu hadin gwiwa sosai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a fannin aikin likitanci.

Tun shekaru 57 da suka wuce kasar Sin ta riga ta fara tura tawagogin kwararrun likitoci zuwa kasashen Afirka. Zuwa yanzu kasar ta riga ta tura likitocinta fiye da dubu 10 zuwa kasashen Afirka, inda suka kula da kuma warkar da majiyyata fiye da miliyan 200.

Cutar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Huldar Hadin Kan Sin Da Afirka Ba

A kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, ana tunawa da labarai da yawa masu burgewa matuka. Misali, a kasar Aljeriya, a loakcin da ake samun barkewar rikici, mutanen kasar sun taba kare likitocin kasar Sin da jikunansu, yayin da aka harbe su da bindiga. A kasar Ghana kuwa, kwararrun kasar Sin sun yi kokarin horar da likitocin kasar, ta yadda aka kafa wata cibiyar aikin tiyatar zuciya mafi inganci a yammacin nahiyar Afirka. Sa’an nan a kasar Comoros, likitocin kasar Sin sun kwashe shekaru kusan 10, inda suka kawar da cutar zazzain cizon sauro baki daya daga kasar.

Duk wadannan batutuwa sun shaida kauna da zaumunci masu zurfi da suka kasance tsakanin Sinawa da jama’ar kasashen Afirka. A lokacin da ake fama da matsala, suna kokarin rufa wa juna baya. Kana muna sa ran ganin a lokacin da yanayin duniya ya samu sassauci, jama’ar kasar Sin da ta kasashen Afirka za su kara kokarin hadin gwiwa, don raya kasashensu tare. (Bello Wang)

Bello