logo

HAUSA

Matakai marasa ma’ana na Pompeo ba za su iya kawar da makomar dangantakar Sin da Amurka ba

2020-12-11 21:18:03 CRI

Matakai marasa ma’ana na Pompeo ba za su iya kawar da makomar dangantakar Sin da Amurka ba

Bisa kusantowar karewar wa’adin aikinsa, Mike Pompeo na kara aiwatar da matakai na hauka. A ranar 9 ga wata, lokacin da wannan babban jami'in diflomasiyyar Amurka ya gabatar da jawabi a cibiyar fasaha ta Georgia, ya yi kakkausar suka ga kasar Sin yana mai cewa, wai "Tana sanya guba a manyan makarantun Amurka", sannan ya yi kaurin suna ga MIT da Jami'ar Washington, saboda "karbar tallafi daga kasar Sin" da kuma "mika wuya ga matsin lambar kasar Sin” da dai sauransu.

Dangane da wannan, jami'o'in biyu sun musanta haka da kakkausan lafazi, kuma jami'ar Washington ta yi tir kai tsaye da kalaman nasa, tana cewa "abin kunya" ne kuma "mai ban haushi"!

Matakai marasa ma’ana na Pompeo ba za su iya kawar da makomar dangantakar Sin da Amurka ba

Wannan shi ne sabon fage na nuna adawa da kasar Sin da 'yan siyasan Amurka suka gabatar, wanda Pompeo ya wakilta.

Kamar yadda manazarta da yawa suka nuna, saboda gwamnatin Amurka ta yanzu tana da sauran lokaci kadan a karagar mulki, wasu 'yan siyasa suna kokarin haka ramuka, da kafa shinge ga gwamnati mai zuwa, suna ta yunkurin rage damar kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, ta hanyar nuna karfi ga kasar ta Sin, ta haka suna ci gaba da nasu ra’ayin siyasa, da nufin sake dawowa bayan shekaru hudu.

Ana iya bambanta daidai da kuskure. Babu kasuwar wasan kwaikwayon ta Pompeo da makamantansa. A kwanakin baya, shugabannin jam'iyyun siyasa a Kambodiya, Botswana, Girka da sauran kasashe sun nuna cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta jagoranci kasar wajen cimma manyan nasarori, ba ma kawai kasar Sin ta amfana ba, har ma ta ba da gudummawa ga zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban duniya.

Akwai tabbacin cewa, jam'iyya mai mulki a kasar Sin, wadda jama'ar kasar ke goyon bayanta da gaske, kuma duniya ta yarda da ita, ko wadancan masu wasa kamar yadda Pompeo yake yi za su iya bata sunanta? (Bilkisu)