logo

HAUSA

Me ya sa ake ba da muhimmanci kan tunanin “kafa al’umma mai makomar daya ga dukkanin bil Adama”

2020-12-11 16:06:45 CRI

A yayin wani babban taron MDD da aka yi a kwanan baya, an sake rubuta tunanin “kafa al’umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama” a cikin wani kudurin dake shafar tsaron sararin samaniya can can can. Ma iya cewa, wannan ne karo na “N” da aka rubuta tunanin “kafa al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama” a cikin muhimman kuduran da aka zartas da su a yayin tarukan MDD. Kamar yadda Zhao Lijian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya nuna a yayin wani taron manema labaru da aka shirya a ran 9 ga watan Disamban, cewar wannan ya yi cikakken bayanin cewa, tunanin “kafa al’umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama” ya riga ya samu karbuwa sosai a duk fadin duniya. Yau, bari mu tabo dalilin da ya sa yanzu ake mai da hankali sosai ga tunanin “kafa al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama”.

Me ya sa ake ba da muhimmanci kan tunanin “kafa al’umma mai makomar daya ga dukkanin bil Adama”

Ma’anar tunanin “kafa al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama” ita ce, ya kamata kowace kasa wadda ke kokarin kiyaye moriyarta, ta kuma girmama halaltacciyar moriyar sauran kasashen duniya, ta yadda a lokacin da take cimma burinta na neman ci gaba, za a iya tabbatar da ganin sauran kasashen duniya ma sun samu ci gaba tare.

Kasar Sin ce ta gabatar da wannan tunani na “kafa al’umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama”. A cikin littafin mai suna “Kasar Sin na neman ci gaba cikin lumana” da aka wallafa shi a shekarar 2011, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da cewa, ya kamata a fito da tunanin bunkasa “al’umma mai makoma daya” a lokacin da ake neman moriyar bai daya ga bil Adama. Sannan a yayin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da aka shirya a watan Nuwamban shekarar 2012, an bayyana karara game da tunanin “kafa al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama”.

Bayan Mr. Xi Jinping ya zama babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a watan Nuwamban shekarar 2012, ya sha nanata wannan tunani. Alal misali, a lokacin da yake ganawa da bako karo na farko bayan ya zama babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar, ya bayyana cewa, yanzu gamayyar kasa da kasa ta zama tamkar al’umma mai makoma daya. A lokacin da tattalin arziki yake fuskantar yanayi mai sarkakiya da matsalolin da suke shafar duk duniya baki daya, babu wata kasa za ta iya kare moriyarta ita kanta. A ran 23 ga watan Maris na shekarar 2013, a lokacin da yake gabatar da jawabi a kwalejin koyon ilmin dangantakar kasa da kasa ta Moscow dake kasar Rasha, ya bayyana wa duk duniya ra’ayin kasar Sin game da makomar wayin kai na bil Adama gaba daya. Bugu da kari, a lokacin da yake ziyartar kasar Tanzania a watan Maris na shekarar 2013, Xi Jinping ya nuna cewa, “Kasashen Sin da Afirka a kullum suna cikin al’umma mai makomar bai daya. Suna da tarihi iri daya, suna kuma kokarin neman ci gaba iri daya, har ma suna da moriya na dogon lokaci iri daya, dukkansu sun hada mu tare.” Daga shekarar 2013 zuwa yanzu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sha ambaton tunanin kafa “al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama” a muhimman bukukuwa ko taruka da yawa, har ma yana kokarin kyautata da kuma kara yin bayanai a ciki. Sakamakon haka, tun daga shekarar 2018, wannan tunani ya fara samun karbuwa daga dimbin al’ummun kasashe da yawa, an kuma sha rubuta shi a cikin muhimman takardun MDD.

Me ya sa ake ba da muhimmanci kan tunanin “kafa al’umma mai makomar daya ga dukkanin bil Adama”

Kokarin kafa “al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin Bil Adama” ya kasance tamkar “shirin kasar Sin” da shugabannin kasar Sin suka gabatar bisa shawarar da suka yanke kan makomar bil Adama. Dukkan kasashen duniya na kasancewa a duniyarmu guda sabo da bil Adam na da duniya daya tilo.

Yanzu duniyarmu ta kasance tamkar wani kauye sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya, da bayanan da ake samu cikin sauri da sauki sakamakon ci gaban fasahar zamani. A don haka, dole ne a yi watsi da tunanin “wani bangare daya dake neman samun riba” tsakanin kasa da kasa, bai kamata a nemi moriya da hankali ba zai dauka ba, a waje daya kuma wani ma ba za iya samun kome ba. Muddin kowace kasa ta mai da hankali kan moriya da adalci a lokacin da take neman ci gaba, to, za a iya samun daidaito tsakanin moriya da adalci a tsakanin kasa da kasa.

Kuduri game da tsaron sararin samaniya dake shafar tunanin kafa “al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama” da aka zartas da shi a babban taron MDD a kwanan baya, da kiraye-kirayen tinkarar annobar COVID-19 da kasashen duniya suka yi, sun bayyana cewa, yanzu yawancin kasashen duniya sun gane cewa, tsaron sararin samaniya da yakar annobar, dukkansu kalubaloli ne da bil Adam suke fuskanta tare, babu kowace kasa da za ta iya warware su ita kadai, kuma babu wata kasa da za ta iya yin alwashin cewa “babu ruwanta”, muddin muka yi kokarin kafa “al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama” tare, babu tantama kasashen duniya za su tinkari duk wata matsala da ka iya kunno a kowane lokaci cikin hadin gwiwa. (Sanusi Chen)