logo

HAUSA

Wane tasiri sabon shirin raya kasa na shekaru 5 na Sin zai samar ga duniya?

2020-12-10 19:46:26 CRI

Wane tasiri sabon shirin raya kasa na shekaru 5 na Sin zai samar ga duniya?

Masu hikama na cewa, “In gani a kasa” wai ana biki a gidan su kare. Ko shakka babu, kasa da kasa suna cin moriyar alfanun dake tattare da manufar kasar Sin na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje tun bayan kaddamar da manufar a shekaru sama da 40 da suka gabata. Tun a shekarun 1978 bayan kaddamar da manufar karkashin jagorancin marigayi Deng Xiaoping, duniya ta ga manyan sauye-sauye masu tarin yawa, kama daga fannin ciniki da tattalin arziki, raya ilmi, yaki da talauci, inganta fasahohi, da kyautata zaman rayuwar al’umma da makamantansu.

Ko da yake, shirye shiryen raya kasa na kasar Sin na gajeren zango, dogo, da kuma matsakaicin zango sun amfanawa duniya matuka. Alal misali, a bisa ga bayanan da mahukuntan kasar suka bayyana a kwanan nan, akwai yiwuwar kasar Sin za ta kara bude kofarta da karfafa kirkire-kirkire cikin shekaru 5 masu zuwa, lamarin da zai samar da sabbin damammaki ga hadin gwiwar kasa da kasa. Kamar yadda shugaban cibiyar binciken harkokin kudi ta jami’ar Tsinghua ta kasar Sin, mista Zhu Min, ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar cikin wannan mako. Zhu Min ya ce yayin da habaka sayen kayayyaki a cikin gida ke da muhimmanci ga gwamnati cikin shekaru 5 masu zuwa, kofar kasar za ta ci gaba da kasancewa bude a wani bangare na shirin inganta kamfanonin kasar, ta yadda za su kara shiga kasuwannin duniya da habaka amfani da kayayyaki a cikin gidan kasar.

Ya ce ana sa ran kasar Sin za ta jagoranci bude kofa a wani babban mataki cikin shekaru 5 masu zuwa, tare da kara jan hankalin masu zuba jari daga ketare. Zhu Min ya kara da cewa, yayin da kasar ke yunkurin bunkasa tattalin arzikin zamani, ana kara bukatar hidimomin bangaren fasahar zamani, wanda ke kara hadin gwiwa tsakanin kamfanoni domin cimma wadannan bukatu. Batun mu’amalar Sin da kasashen Afrika al’amari ne mai muhimmanci matuka, mista Zhu ya yi tsokaci cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da kasashen Afrika a bangaren raya wadancan hidimomi da taimakawa bunkasa kanana da matsakaitan harkokin kasuwanci. Taron dai wanda cibiyar bincike kan harkokin cinikayya tsakanin Sin da kasashen duniya ta shirya ya samu halartar jakadu da manyan jami’an diflomasiyya da ’yan kasuwar kasa da kasa, ko da yake, dama an ce, “Juma’a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta. (Ahmad Fagam)