logo

HAUSA

Jami’an diflomasiyya na Habasha da Zimbabwe dake nan kasar Sin: Jari daga kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga kasashensu

2020-12-10 13:46:05 CRI

Jami’an diflomasiyya na Habasha da Zimbabwe dake nan kasar Sin: Jari daga kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga kasashensu

A kwanan baya, bi da bi ne jakadan kasar Habasha dake nan kasar Sin Teshome Toga Chanaka da jami’in dake kula da ofishin jakadancin kasar Zimbabwe dake kasar Sin Mr. Mqabuko Spencer Dube, sun yi hira da wakiliyarmu, inda suka yaba da alkawarin da shugaban kasar Sin ya dauka na “mayar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a matsayin kayan da al’ummomin kasashe daban daban za su iya yin amfani da ita gwargwadon karfinsu.” Jami’an sun kuma jaddada cewa, jari daga kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga kasashen Afirka, ciki har da kasashen Habasha da Zimbabwe, a don haka, suna sa ran za a kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, suna kuma maraba da karin masu zuba jari daga kasar Sin. Ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

Bana shekaru 50 ke nan da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Habasha. Jakada Teshome Toga Chanaka na kasar Habasha dake nan kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin ita ce kasar dake kan gaba wajen zuba jari a kasar Habasha, kuma muhimmiyar kasuwa da ake fitar da kayayyaki kirar kasar Habasha.

“Kasar Sin ta kasance muhimmiyar kasar dake zuba jari kan ayyukan more rayuwar al’umma a kasar Habasha. Sannan kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin, su ma sun zuba jari a masana’antun samar da kayayyaki da yawa a kasar Habasha. Bugu da kari, kasar Sin ta samar wa Habasha dimbin taimako da rance mai rangwamen kudin ruwa. Wadannan jari da rance sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki da kayayyakin more rayuwar al’umma na Habasha.”

Teshome Toga Chanaka ya nanata cewa, jari daga kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga ci gaban kasar Habasha. Sakamakon haka, ya yi watsi da wasu zarge-zargen da wasu kasashen yammacin duniya suke yi wa kasar Sin kan batun basusuka da wasu kasashen Afirka suke ci. Mr. Teshome ya ce, “Ina da tambayoyi biyu da nake bukatar amsa daga wadannan kasashen yammacin duniya, da farko, ko kasashenmu na Afirka, kamar Habasha a wajen kasar Sin kawai muka ari kudi? A’a, ba haka ba ne. Wasu hukumomin kasa da kasa, kamar Bankin Duniya da asusun ba da lamuni na duniya IMF, su ma suna ba mu rance. Bugu da kari, muna kuma samun rance daga sauran kasashen duniya. Sabo da haka, don me, a kullum kuke zargin kasar Sin kawai? Tambayata ta biyu ita ce, don me muka nemi rance? Mun nemi rance daga wajen kasar Sin ne domin zuba jari a fannonin samar da kayayyaki da ayyukan more rayuwar al’umma. Mun yi daidai wajen zuba jari. Mun samu kyakkyawan sakamako daga bunkasar tattalin arzikin Habasha cikin sauri.”

Jami’an diflomasiyya na Habasha da Zimbabwe dake nan kasar Sin: Jari daga kasar Sin yana da muhimmanci sosai ga kasashensu

A nasa bangare, Mr. Mqabuko Spencer Dube, jami’in kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Zimbabwe yanzu ya gaya wa wakiliyarmu cewa, yana jinjinawa taimakon da kasar Sin ta samar wa kasarsa wajen dakile annobar COVID-19.

A shekarar 2019, kasar Zimbabwe ta gamu da bala’in fari mai tsanani da bala’in mahaukaciyar guguwa, sannan a shekarar 2020, ta gamu da matsalar annobar COVID-19. Mr. Mqabuko Spencer Dube ya bayyana cewa, kasar Zimbabwe ta yi nasarar dakile kalubaloli iri iri, haka kuma kasar Sin ta samar wa kasar Zimbabwe taimako ba tare da son kai ba. Kasar Zimbabwe na yi wa kasar Sin godiya kwarai.

“Muna jinjinawa kasar Sin sabo da taimakon da ta samarwa kasarmu wajen dakile annobar COVID-19. Ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta samar mana kayayyakin kandagarkin annobar ba, har ma ta tura kwararrun kiwon lafiya zuwa kasarmu, sun bayar da gudummawa kwarai.”

A nan gaba, kasar Sin za ta hanzarta bunkasa tattalin arzikinta bisa bukatun da ake da su a kasuwannin cikin gida da na ketare tare. A tsakiyar watan Nuwamban bana, kasar Zimbabwe ta fitar da sabon shirinta na neman bunkasuwa, inda ta ce, za ta tabbatar da ganin tattalin arzikinta ya karu da 5% a duk shekara a cikin shekaru biyar masu zuwa, sannan ya zuwa shekarar 2030, za ta zama kasa mai matsakaiciyar wadata. Sakamakon haka, Mr. Dube ya ce, yana fatan masu zuba jari na kasar Sin za su kara zuba jari a kasar Zimbabwe. Yana mai cewa, “Muna bukatar karin jarin waje. Za mu kara kokari don cimma burin mu na bunkasar kasar Zimbabwe, ta yadda a shekarar 2030, kasar za ta zama mai matsakaiciyar wadata a duniya.” (Sanusi Chen)