logo

HAUSA

Amurka Za Ta Fuskanci Kiyayya Daga Bangarori Daban Daban Domin Cin Zalin Da Ta Yiwa Kasa Da Kasa A Fannin Siyasa

2020-12-09 13:21:15 CRI

Amurka Za Ta Fuskanci Kiyayya Daga Bangarori Daban Daban Domin Cin Zalin Da Ta Yiwa Kasa Da Kasa A Fannin Siyasa

Jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi zargin da bai dace ba kan dokar kare tsaron kasa ta yankin Hong Kong da kasar Sin ta tsara da kuma aiwatarwa, sa’an nan, ya sanar da kakaba wa mataimakan shugabannin kwamitin koli na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin takunkumi. Lamarin da ya saba wa tsarin kwamitin koli mai tsara dokoki na kasar Sin, da ma ka’idojin cudanyar kasa da kasa, kuma, ya kasance mataki mai tsanani na tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, wanda ya bata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, saboda yadda Amurka ta ci zalin kasar Sin a fannin siyasa. Tabbas, kasar Sin za ta mayar da martani, domin kare ‘yancin kai da burinta na neman ci gaba.

A watan Yunin bara, yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya shiga yanayin tashin hankula, sabo da wutar da wasu kasashen ketare suka rura don neman raba yankin Hong Kong da kasar Sin. Shi ya sa, kwamitin koli na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin ya tsara dokar kare tsaron kasa dake da nasaba da yankin Hong Kong domin shimfida zaman lafiya a yankin da tabbatar da bunkasuwar yankin yadda ya kamata, wadda ta samu karbuwa daga wajen al’ummomin yankin Hong Kong.

Mike Pompeo da wasu ‘yan siyasar kasar Amurka sun kakabawa jami’an kasar Sin takunkumi domin hana aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong, da kuma bata tsarin “Kasa daya, mai tsarin mulki biyu”, ta yadda, za su hana bunkasuwar kasar Sin. A sa’i daya kuma, suna son haddasa matsaloli ga sabuwar gwamnatin kasar Amurka a fannin farfado da dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasar Sin.

Amma, tsarin “kasa daya mai tsarin mulki biyu” yana da tushe mai zurfi a yankin Hong Kong, yadda kasar Amurka take neman bata tsarin ba zai hana al’ummomin yankin shimfida kwanciyar hankali da neman ci gaba ba, balle ma farfadowar kasar Sin baki daya. Kana, Matakan da kasar Amurka ta dauka sun harzuka al’ummomin kasar Sin, wadanda suka kuma karfafa aniyar kasar ta kare tsaro da ci gaban yankin Hong Kong. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)