logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin cika alkawarinta kan alluran rigakafin COVID-19

2020-12-09 20:42:56 CRI

Kasar Sin na kokarin cika alkawarinta kan alluran rigakafin COVID-19

A cewar rahotanni daga kafofin yada labarai na Hadaddiyar daular Larabawa, ma’aikatar lafiya da rigakafin kasar ta sanar a yau Laraba, cewa ta yi rajistar a hukumance da allurar rigakafin COVID-19 da rukunin kamfanin Sinopharm na kasar Sin mai hada magunguna ta samar.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kashi na biyu na allurar rigakafin COVID-19 miliyan 1 daga kasar Sin sun isa Sao Paulo na kasar Brazil, kuma kashin farko na allurar rigakafin COVID-19 miliyan 1 da dubu dari 2 daga kasar Sin ya isa Jakarta, babban birnin kasar Indonesia……

"Za mu cika alkawuranmu na samar da taimako da goyon baya ga sauran kasashe masu tasowa, da kuma kokarin sanya alluran rigakafin kasancewar wani abu da jama'a za su iya amfani da shi, kuma za su iya biyan kudin amfani da shi." Wannan ne ra’ayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin taron koli na G20 da aka yi kwanan nan.

Yanzu haka, tare da kyakkyawan ci gaban da kasar Sin ke kara samu game da nazari da habaka alluran rigakafin, wannan hangen nesa na kasar Sin yana kusan zama gaskiya.

Amma, ko yaushe akwai wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na yammacin duniya, wadanda ba sa iya ganin ci gaba da kasar Sin ke samu a fannin alluran rigakafin, da kuma gudummawar da kasar ta bayar ga duniya, suna ta bata sunan kasar Sin, kana suna yada jita-jitar cewa kamar "Kasar Sin na mayar da allurar rigakafin a matsayin kayan aikin siyasa", da "satar fasahohin kasashen yamma na nazari da habaka alluran" da dai makamancinsu.

Ga misalin, a yayin da allurar rigakafin kasar Sin ta isa kasar Indonesiya, jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya, ta yi karya a wani rahotonta cewa, wai "akwai hadari idan an yi amfani da allurar rigakafin kasar Sin,  saboda an sanya dalilan siyasa a ciki."

Kamar yadda wasu manazarta suka nuna, ana ta fito da kalaman bata sunan alluran rigakafin kasar Sin ne, sakamakon yunkurin siyasa da ma mallakar kasuwa mai girma ga alluran rigakafin na yammacin duniya. Ga wadancan kasashe masu neman dabarar yaki da annobar, samun alluran rigakafi masu inganci, da amfani, na da mahimmancin gaske, dole ne kuma a bi tsauraran matakan bincike su.

Alluran rigakafin da kasar Sin ta samar sun samu karbuwa daga wasu muhimman kasashe abokantaka, kuma wannan ya mai da martani mai karfi kan wadancan jita-jita. (Bilkisu)