logo

HAUSA

Yawan kayayyakin shige da fice na Sin ya ci gaba da samun karuwa cikin watanni shida a jere

2020-12-08 14:34:55 CRI

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da wasu alkaluma a jiya Litinin, wadanda ke nuna cewa, a watanni 11 na farkon shekara nan, darajar cinikayyar kayayyakin kasar, ta kai Yuan triliyan 29.04, karuwar kaso 1.8 kan makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, kana yawan kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya ci gaba da samun karuwa cikin watanni shida a jere. Masana sun bayyana cewa, akwai yiwuwar zai kiyaye cinikayyar wajen kasar a dukkan shekarar bana.

Bisa sabuwar kididdigar da aka yi, a watan Nuwamban bana, yawan kudin da aka samu daga kayayyakin fice da shige na kasar Sin ya kai Yuan triliyan 3.09, wanda ya karu da kaso 7.8 bisa na makamancin lokacin bara, a cikinsu, yawan kudin kayayyakin da aka fitar ya kai Yuan triliyan 1.8, wanda ya karu da kaso 14.9 kan na shekarar da ta gabata, kuma yawan kayyayakin da aka shigo da su ya kai Yuan triliyan 1.29, wanda ya ragu da kaso 0.8 bisa na shekarar bara. Shugaban ofishin nazari na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Li Kuiwen ya bayyana cewa,“Tun daga farkon bana, cutar COVID-19 take yaduwa a fadin duniya, lamarin da ya haifar da raguwar tattalin arzikin duniya sosai, amma Sin ta dauki matakan kandagarkin cutar, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kuma matakan kiyaye cinikayyar waje sun yi da amfani, yawan kayayyakin shige da fice na Sin ya yi ta samun karuwa a jere tun daga watan Yunin bana, ta hakan kasar ta kara shiga kasuwar duniya.”

Bisa kididdigar da aka yi kan watanni 11 na farkon bana, yawan kayayyakin da aka fitar ko shigar da su a tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN, da EU, da kasar Amurka, da Japan, da Koriya ta Kudu ya ci gaba da karuwa. A cikinsu, kasashe membobin kungiyar ASEAN sun fi yin cinikayya da kasar Sin, yawan cinikayyar da aka yi a tsakaninsu da Sin ya karu da kaso 6.7 cikin dari, wanda ya kai kaso 14.6 bisa daukacin cinikayyar waje ta kasar Sin. EU ce a matsayi na biyu, wato yawan cinkayyarsu ya kai kaso 14, inda Amurka ta zama na uku, da kaso 12.6. Babbar manajar kamfanin kimiyya da fasaha na Jinjin na Shenzhen Lin Lihua ta bayyana cewa,“Yaduwar cutar COVID-19 ta canja hanyoyin rayuwar jama’a, mutane da dama sun rage fita waje, kananan na’urorin amfanin gida kamar na’urar kofi sun fi samun karbuwa a kasashen waje. Tun daga farkon bana, kamfaninmu ya fitar da na’urorin kofi fiye da dubu 180 zuwa kasar Italiya, wanda ya karu da kaso 20 bisa makamancin lokacin bara.”

Tun daga shekarar bana, sakamakon cutar COVID-19, an samu babbar illa ga cinikayyar kayayyakin shige da fice ta kasa da kasa na duniya. Amma Sin ta dauki wasu matakan kiyaye cinikayyar waje cikin nasara, da taimakawa kamfanoni da dama wajen warware matsalolinsu. Direktan cibiyar nazarin hadin gwiwar tattalin arziki a yankuna ta ma’aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin Zhang Jianping ya bayyana cewa,“Tun daga farkon shekarar bana zuwa yanzu, an fuskanci babban canji kan cinikayyar waje. Daga farko ba mu iya kammala kwangilar samar da kayyayaki ba, sai kuma rashin samun kwangila bayan mun dawo bakin aiki, yanzu kuma muna samun karuwar cinikayyar waje. Mun samu wannan sakamako mai kyau ne saboda daukar matakan kiyaye cinikayyar waje, musamman rage haraji da samar da goyon baya ga kamfannonin kanana da matsakaita, matakan sun taimakawa kamfanonin masu amfani da jarin waje warware matsalolinsu.”

Zhang Jianping ya bayyana cewa, abu mai wuya ne a samu kyakkyawan sakamako kamar hakan, akwai yiwuwar Sin ta ci gaba da samun karuwar cinikayyar waje a dukkan shekarar bana. (Zainab Zhang)