logo

HAUSA

Laifi tudu ne, ka hau naka ka hango na wasu

2020-12-08 17:02:29 CRI

Laifi tudu ne, ka hau naka ka hango na wasu

Kasar Sin ta bayyana cewa, tuni ta cimma burinta na shekarar 2020 a fagen kiyaye muhalli, tun ma kafin lokacin da ta yi tanadin hakan. Kasar ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying, a lokacin da take mayar da martani dangane da ikirarin da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, Keith Krach ya yi cewa, kasar Sin na gurbata muhalli.

Irin wadannan kalamai ba sabon abu ba ne a wajen ’yan siyasar Amurka, inda a ko da yaushe, suke rainawa ko take irin nasarorin kasar Sin tare da nuna mata yatsa ko shafa mata bakin fenti da nufin dakushe farin jininta a duniya.

Amurka a matsayinta na kasar da ta ci gaba kuma mai karfi, ta yi gaban kanta wajen janyewa daga muhimmiyar yarjejeniyar sauyin yanayi da kasashen duniya suka cimma, wadda ke da nufin kiyaye muhalli da rage dumamar yanayi a duniya. Wannan mataki abu ne da ya yi gagarumin cikas ga burin da ake da shi na kiyaye muhalli a duniya.

Laifi tudu ne, ka hau naka ka hango na wasu

Burin kasar Sin a kullum shi ne, samun ci gaba, amma ta hanyar kiyaye muhalli, inda a kullum take mayar da hankali kan makamashi mai tsafta da dasa bishiyoyi da samar da motoci da na’urorin da ba sa gurbata muhalli, lamarin da a ko da yaushe ke samun ci gaba. A daya bangaren kuma Amurka na ta janyewa daga yarjejeniyoyin da suka shafi kiyaye muhalli .

A matsayinta na kasar dake fitar da gurbatacciyar iska mafi yawa a duk duniya, Amurka ta ki amince da yarjejeniyar Kyoto, da ta Basel, wadanda suka zama alamu na kin yarda da daukar matakan kiyaye muhalli, lamarin da ke yi wa ita kanta Amurkar illa, baya ga sauran sassan duniya. Amurka ta janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a lokacin da take tsaka da fuskantar matsalolin muhalli da suka hada da wutar daji da guguwa da sauransu. Ban da haka, matakan nata na nuna ta a matsayin wadda ba za a iya dogaro da ita ba cikin al’amuran da suka shafi duniya, kana kasashen duniya za su gaza amincewa da ita wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a sauran yarjejeniyoyin da suka shafi kasa da kasa.

Kamar yadda Madam Hua ta bayyana, lallai ya kamata Amurka ta binciki kanta kafin ta zargi sauran kasashe, ko da yake, laifi tudu ne, ka hau naka ka hango na wasu. (Faeza Mustapha)

Faeza Mustapha