logo

HAUSA

CMG yana inganta hadin-gwiwa da kamfanin China Mobile

2020-12-08 20:58:21 CRI

CMG yana inganta hadin-gwiwa da kamfanin China Mobile

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta hadin-gwiwa da kamfanin sadarwar China Mobile a yau Talata a birnin Beijing. Kana, an kaddamar da cibiyar watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo masu ingancin gaske, bisa fasahar sadarwar 5G, wadda CMG da China Mobile suka gina tare, abun da ya shaida irin hadin-gwiwar da bangarorin biyu suke yi, a fannonin da suka shafi gabatar da shirye-shiryen wasannin motsa jiki na kasa da kasa, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam na AI da sauransu.

CMG yana inganta hadin-gwiwa da kamfanin China Mobile

A wajen bikin daddale yarjejeniyar, shugaban CMG Mista Shen Haixiong ya bayyana cewa, ta hanyar fadada hadin-gwiwa da kamfanin China Mobile, CMG zai kara habaka, daga wata kafar watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin, zuwa wata babbar cibiyar watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin mai inganci a duk duniya.

Haka kuma CMG zai sabunta hanyoyin watsa shirye-shirye, wato daga na gargajiya zuwa zurfafa yin gyare-gyare ga bangaren samar da sabbin shirye-shirye, kana, zai sabunta fasahohin watsa shirye-shiryen na gargajiya, zuwa wasu sabbin fasahohin zamani, ciki har da fasahar sadarwar 5G+4K/8K+AI. (Murtala Zhang)