logo

HAUSA

"Taurarin intanet" na taka muhimmiyar rawarsu, wajen kawar da talauci, da raya al’umma mai matsakaicin karfi

2020-12-08 18:19:49 CRI

"Taurarin intanet" na taka muhimmiyar rawarsu, wajen kawar da talauci, da raya al’umma mai matsakaicin karfi

A cikin kasar Sin dake samun saurin ci gaba a fannin tattalin arziki na “taurari a kafar intanet”, shirin kai tsaye na sayar da kayayyaki ya kasance wata alamar zamani, wadda ke samun karbuwa sosai a nan kasar. Irin alamar dake amfani da dandalin sada zumunta na yanar gizo don tattara dumbin masu sha’awar “taurarin intanet”, tare kuma da canza tasirin masu sha'awar zuwa fa'idodin tattalin arziki, shi ne abin alajabi na zaman al’ummar kasar a yanzu haka.

Bisa wannan yanayin da ake ciki, "taurarin intanet" na taka muhimmiyar rawarsu, wajen kawar da talauci, da raya al’umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni.  Gan Youqin na daya daga cikinsu.  To, masu sauraro, a cikin shirinmu na makon da ya wuce, mun kawo muku kashi na farko game da labarin ta, a yau kuma za mu ci gaba da kawo muku kashi na biyu kan labarin Wannan baiwar Allah.

Bayan nasarar farko da ta cimma, Gan Youqin ta fara yin gajeren bidiyo game da abinci bisa shawarar dan dan uwanta da mijinta. Bidiyon abincin nata ya ja hankali sosai. Daga baya, dan dan uwana ya kara ba ta shawarar ta sauya fasali, don haka suka yi kokarin fadadawa zuwa tsara bidiyo game da rayuwar karkara.

To sai dai fa, akasin mutum sanannen a kafar Intanet, a kauyen su wasu sun rika yiwa Gan Youqin gani-gani.

Sukar da mazauna garin suka yi mata ya sa Gan Youqin ta zama mara taimako sosai, amma ra’ayinsu ya canza bayan da Gan Youqin ta soma aikin sayar da kaya a intanet.

A wancan lokacin, Gan Youqin ta kan sanya yadda take hawan dutse don sakawa bishiyoyi masu 'ya'yan itace taki, da dibar ' ya'yan itatuwa, da kuma dafa abinci da 'ya'yan itatuwa a Intanet. Sannu a hankali, wasu masu sha’awar aikin ta sun rika nuna goya baya ta hanyar saka sakwannin yabo a kasan bidiyon suna cewa: "' Ya'yan itatuwan gidanku suna da kyau, ko za ki iya sayar min da su? " An yi ta yin tambayoyi iri-iri wadannan, dana nan ne kuma sai Gan Youqin ta shirya bude wani shagon yanar gizo, don sayar da kayayyakin gargajiya na garinsu.

A watan Oktoban shekarar 2017, shagon ta ya fara karbar odar 'ya'yan itatuwa. A cewar Gan Youiqin, "Idan zan iya sayar da kilo dubu 10, zan yi matukar farin ciki."

Abin da Gan Youqin ba ta yi tsammani ba shi ne, bayan ta samar da tallace-tallacen odar na mako guda, wadanda suka yi odar za su kai masu bukatar kusan kilo 50,000, adadin da gaba daya ya wuce tunaninta. Ta ce, "A wancan lokacin, na yi farin ciki tare kuma da damuwa, saboda 'ya'yan itacen da iyalina ke da su ba su wuce 25,000 zuwa 30,000 ba. Daga baya, na tattauna da mazauna kauyen, don na sayar da' ya'yan itatuwansu tare da nawa."

Saboda wannan mataki mai ban mamaki ne, yan kyauyen suka sake nazari kan wannan mace: Tana tambayar kan su shin me ya sa take da kyakkyawar kasuwa? Mutuniyar na iya sayar da dukkan 'ya'yan itace ta hanyar magana da hira a gaban wayar salula kawai?

"Taurarin intanet" na taka muhimmiyar rawarsu, wajen kawar da talauci, da raya al’umma mai matsakaicin karfi

Cunkoson ababen hawa a kauyen da Gan Youqin take bai dace ba, hanya daya tilo ta sayar da 'ya'yan itace ita ce babbar kasuwa dake gundumar. Manoma, suna diban 'ya'yan itace da rana, kuma suna safarar su zuwa kasuwar dare don su sayar. Idan farashin kasuwa bai yi kyau ba, mai sayar da ‘ya’yan itacen zai sa farashin ya yi kasa.

Gan Youqin ta bayyana cewa, "Ta hanyar intanet, yana da matukar sauki a sayar da 'ya'yan itatuwa. Muna debo ‘ya'yan itatuwa da rana, sai mu tattara su, mu kuma tura su zuwa duk sassan kasar da yamma. Ba wai kawai ban damu da sayar da 'ya'yan itacen da na shuka ba ne, har ma ana sayar da dukkan ' ya'yan itacen da ke kauyenmu." Gan Youqin ta yi farin ciki da cewa, "Ganin irin wadannan sauye-sauyen, matasa da yawa sun zabi komawa garinmu don yin kwangilar lambu, saboda wannan ya ninka yawan kudaden da suke samu daga yin aiki a waje."

Daga baya dai, sai Gan Youqin ta soma amfani da dandamalin sabbin kafofin watsa labaru, da tasirin talla ta a zamantakewar al’umma, don kara mu’amala da waje, da nufin kara fadada tallace-tallace na kayayyakin amfanin gona na wurin.

Ya zuwa karshen shekarar 2018, Gan Youqin ta bude tashoshin cinikayya ta intanet a sanannun dandamali na sayar da kaya ta intanet sama da guda 20 a duk fadin kasar. A waje guda kuma, ta karbi wakilan tallace-tallace na kayan amfanin gona 1,000 a duk faɗin kasar.

A karkashin jagoranci, da tallafi daga sassan da abin ya shafa na gwamnatin wurin, Gan Youqin ta samar da guraban ayyukan yi sama da 60 kai tsaye ga garinsu, wanda suka shafi mutane sama da 200.

Daga watan Yuli zuwa Disamba na shekarar 2019, a karkashin jagorancin gwamnati, Gan Youqin ta hada kai da wasu kamfanoni masu kauna, suka samar da kananan kaji, da agwagi, da 'ya'yan itace da dai sauransu, wadanda darajar su ta kai kudin Sin RMB yuan 200,000, ga iyalai masu fama da talauci sama da 1,500. A lokacin ne kuma suka sanya hannu kan yarjejeniyar saya don tabbatar da farashin kaya, hakan ya taimaka wajen kawar da talauci daga tushe da kuma asali.

A cikin shekarar 2019, ta hanyar sayar da kaya ta intanet ne, Gan Youqin ta taimaka wa garinta, sayar da kayan amfanin gona sama da kilo miliyan 6, masu darajar sama da yuan miliyan 34.

Gwargwadon kwarewa, gwargwadon nauyin da zai wajaba a dauka. Abin da Gan Youqin ba ta yi tsammani ba shi ne, kirkirar gajeren bidiyon da ta  yi domin "nishadi" a farko, zai zame nata kasuwanci wanda ke samun bunkasuwa a yanzu haka.

Abin da ya kara zame musu yanayin bazata shi ne, ta hanyar daukar karamin bidiyo, da sayar da kaya a intanet, Gan Youqin da mazauna kauyen sun sami wani dandamali na cimma burinsu, har ma da bude wani sabon tsarin zirga-zirgar kayayakin amfanin gona, wadda ta karawa wurin kwarin gwiwar kawar da talauci ta hanyar raya sana’a.

A lokaci guda, hakan ya kawo mata karamci mai yawa, kamar su: lambar yabo ta "Mutanen Kasa a fannin aikin noma na 2018”, da ta "Mutane Mafi Taka Rawa Kan Karuwar Kudin Shiga", da ta "Mafi Kyawun Iyali", da kuma ta "Manyan Mutane Goma A fannin Sayar Da Kaya A Intanet" da dai sauransu.

Kamar yadda ta rubuta a cikin gabatarwar ta a dandalin ta na bidiyo: Kasance mai gaskiya, zama mutuniya mai daraja. Wannan shi ne bayani mafi dacewa da ta wallafa game da halinta.

Bilkisu