Yaki da talauci a jihar Xinjiang
2020-12-07 19:57:58 CRI
Kamar dai yadda Bahaushe kan ce, “Da ruwan ciki a kan ja na Rijiya”, wato abu ne mawuyaci bil Adama ya rayu rayuwa mai inganci, har ya amfani kan sa da ma sauran al’umma, ba tare da ya samu muhimman abubuwan bukatun rayuwa kamar abinci, da kiwon lafiya, tsaro da ilimi tun daga tushe ba. Rashin wadannan abubuwa muhimmai, kan haifar da gurbacewar rayuwa, da rashin tsaro, da rashin samun ci gaba tsakanin al’umma.
Lura da haka ne kuma, ya sanya mahukuntan kasar Sin suka bullo da tsare-tsare daban daban, na yaki da fata, da sada al’ummun yankunan kasar daban daban da ababen more rayuwa. Karkashin manufar yaki da talauci, kasar Sin ta yi rawar gani wajen kulla alakar kamfanoni masu jarin kan su, da manoma, ko mazauna kauyuka dake yankuna marasa wadata, ta yadda irin wadannan kamfanoni za su samar da guraben ayyukan yi, da kuma horo na koyon dabarun noma ko sana’o’i na zamani, ta yadda sassan biyu za su ci gajiya daga juna.
Misalin hakan ya bayyana a zahiri a jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin Sin, inda a baya bayan nan, na ganewa idanu na ci gaban da yankin Hotan dake jihar ta Xinjing ya samu a wannan fanni.
Da farko, cikin jerin irin wadannan manufofi, gwamnatin kasar Sin ta taimaka wajen sake ginin unguwar Hotan Tuancheng dake yankin Hotan, inda bayan shekaru 4 unguwar ta sauya zuwa ta zamani, mai cike da gine gine da aka kawata da salon ginin al’ummar Uygur, wanda hakan ke jawo hankulan masu yawon bude ido.
Kaza lika an inganta yanayin yankunan Hamadar Takla Makan dake wannan yanki, Hamada mafi girma a dukkanin kasar Sin, kuma ta biyu a duniya bayan Hamadar Sahara, wanda hakan ya samar da wata dama ta amfani da Rakuma domin nishadantar da masu zuwa kallon Hamadar da yawon bude ido.
Har ila yau, an kafa kamfanin noman lemar kwadi a gundumar Moyu dake Hotan, inda mazauna wurin da dama suka samu damar fita daga kangin talauci, sakamakon raya sana'ar noman lemar kwadin da suka runguma.
Kaza lika, a kauyen Tuohula dake gundumar ta Hotan, akwai wani karamin kamfanin sayar da amfanin gona mai suna Lvbao, mallakar malam Mamati Abdullah. Malam Mamati ya cimma nasarar kafa wannan kamfani ne cikin watan Afrilun shekarar 2019, bayan samun horo a fannin na'ura mai kwakwalwa da ilimin kasuwanci. Wannan kamfani ya samu kafuwa ne da tallafin kudaden da gwamnati ta samar gare shi. Kuma bayan kafuwar kamfani zuwa yanzu ya samu ribar da ta kai RMB dubu 700.
Baya ga ribar da yake samu, mai kamfanin ya samar da guraben ayyukan yi ga karin mazauna wannan kauye. Kaza lika kamfaninsa yana karbar oda ga masu saye, da kuma karbar kayan lambu nau'o’i daban daban daga manoma, wanda hakan ke tabbatar da cewa manoma ba su yi asarar amfanan gona da suke nomawa ba.
Bugu da kari, akwai kamfanin kiwo da sarrafa kaji na Meibite dake kauyen Sayibage a gundumar Moyu, da kamfanin sarrafa naman Agwagi na Litianxiangnong, wadanda duka na taimakawa yaki da fatara.
Ga misali, kamfanin Litianxiangnong yana da ma'aikata 570 wadanda suka fita daga kangin talauci sakamakon guraben ayyukan da ya samar musu. Yana kuma iya sarrafa naman Agwagi har miliyan 20 a shekara guda. Har ila yau kamfanin na samarwa mazauna kauyukan dake wannan yanki damar kiwata kananan Agwagi da yake samar musu kyauta, wadanda yawansu ke haura miliyan 12 a duk shekara, kana ya saya daga wurin su idan Agwagin sun girma. Kamfanin Litianxiangnong da manoman yankin na hadin gwiwar kafa rumfunan kiwo masu cin agwagi 5000.
Kamfanonin biyu sun zama jigon samar da guraben ayyukan yi ga mazauna wannan yanki, wanda tabbas hakan wata muhimmiyar hanya ce ta yaki da fatara, da inganta samar da nama, da samar da riba ga masu zuba jari. Kana hanyar raya yankunan da suke baya baya ta fuskar ci gaba.
Da yake yaki da talauci bai tsaya ga samar da sana’o’i, ko guraben ayyukan yi kadai ba, a Hotan an raya harkar kiwon lafiya, da kula da asibitoci tun daga matakin unguwanni, da kauyuka, da garuruwa, ta yadda mazauna yankuna masu nisa ke iya samun damar ganin kwararrun likitoci cikin sauri, ba kuma tare da sun tafi wurare masu nisa ba, ta amfani da yanar gizo, karkashin wani salo na hadin gwiwar manya da kananan asibitoci.
A bangaren damar gudanar da addinai, na ganewa idanu na yadda mabiya addinin musulunci ke gudanar da sallah, a babban masallacin Kuonaxiehai'er dake gundumar Moyu na Uygur, da masallacin Jiaman dake yankin Hotan wanda ke da tarihin shekaru 145 da kafuwa.
Muna iya cewa, kafin mutum ya gaskata kafofin dake yada labarun sukar kasar Sin game da harkokin addinai, da ’yancin ’yan kwadago, ya dace ya bibbiyi rahotanni na ganau, dake tantance ainihin halin da wannan yanki na Xinjiang ke ciki.
Bahaushe kan ce “Gani ya kori Ji”, don haka bisa bayanai da bidiyo tare da hotunan da muka gabatar, muna iya fahimtar irin jajircewar gwamnati da jama’ar kasar Sin, wajen daukar matakai daki-daki tare, domin yakar fatara, da kuma kyautata damar bin addinai daban daban, ba tare da wata tsangwama ba. (Saminu Hassan)