logo

HAUSA

Ibrahim Mansur Abulfathi: Dalibin Najeriya dake nazarin sufurin jiragen kasa a kasar Sin

2020-12-06 19:40:56 CRI

Ibrahim Mansur Abulfathi: Dalibin Najeriya dake nazarin sufurin jiragen kasa a kasar Sin

Kwanan nan, Murtala Zhang ya zanta da Ibrahim Mansur Abulfathi, ko kuma Quan Xiaobao a yaren Sinanci, wani dalibi ne dan Najeriya wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin.

Ibrahim Mansur Abulfathi, wanda ya yi shekaru shida yana karatu da aikin kasuwanci a biranen Jinzhou da Guangzhou da kuma Changsha na kasar Sin, ya ganema idanunsa yadda kasar ta samu ci gaba a fannonin rayuwar al’umma da sauransu. Sa’annan ya ce, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin gudu, har ma Sin da Najeriya suna hadin-gwiwa sosai a wannan fanni. Burinsa shi ne bayan ya kammala karatu a kasar Sin, yana son bayar da gudummawarsa ga gina kasar Najeriya musamman a fannin zirga-zirgar jiragen kasa da kuma sufurin kayayyaki.(Murtala Zhang)