logo

HAUSA

Tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da kasashen Afirka

2020-12-06 17:38:29 CRI

Tabbatar da kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da kasashen Afirka

A ranar 4 ga wata, manzon musamman na shugaban kasar Sin, wanda kuma shi ne mamban majalisar gudanarwar kasar kana ministan harkokin waje na kasar ta Sin, Mr. Wang Yi, ya halarci babban taron “hadin gwiwar MDD da tarayyar Afirka” da kwamitin sulhun majalisar ya shirya ta yanar gizo, inda ya gabatar da jawabi.

A jawabin da ya gabatar, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, yaduwar annobar Covid-19 ta haifar da sabbin kalubaloli ga kasashen Afirka ta fannonin siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al’umma da zaman lafiya da kuma tsaro, kamata ya yi MDD ta gaggauta daukar matakai, don taimakawa kasashen daidaita matsalar da suke fuskanta.

Dangane da wannan, Mr. Wang Yi ya kuma gabatar da wasu shawarwari hudu. Na farko shi ne a yi kokarin tallafawa kungiyar tarayyar Afirka wajen tsara dabarun yaki da annobar a fadin nahiyar ta Afirka, sa’an nan, a tabbatar da kasashen Afirka suna iya samun alluran rigakafin annobar yadda ya kamata. Baya ga haka, a goyi bayan kasashen Afirka wajen inganta tsarin kiwon lafiya da kyautata kwarewarsu wajen tinkarar munanan cututtuka masu yaduwa. Na biyu shi ne, a tallafawa al’ummar kasashen Afirka wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashensu, saboda in babu kwanciyar hankali a Afirka, lalle da wuya a tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya. Na uku, a karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka ta fannonin aikin gona da ilmantarwa da kiwon lafiya da kuma gina manyan ababen more rayuwa, don cimma muradun samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, tare da tallafawa kasashen Afirka su gina yankin ciniki maras shinge da saukaka illolin da annobar Covid-19 ke haifarwa ga tattalin arzikinsu. Na hudu, ya kamata a kara inganta tsarin yadda harkokin duniya ke gudana, tare da daidaita matsalolin rashin samun adalci ta fannoni daban daban. Kamata ya yi MDD ta kara yin la’akari da bukatun kasashen Afirka da moriyarsu a yayin tsara ka’idoji da raba albarkatu da kuma daukar ma’aikatanta, ta yadda za a kara wakilcinsu a majalisar.

A hakika, kullum kasar Sin ta kasance sahihiyar aminiyar kasashen Afirka, wadda kuma take kokarin taimakawa kasashen Afirka cimma burin ci gabansu. Domin tallafawa kasashen Afirka dakile yaduwar annobar Covid-19, shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya ba da shawarar kiran taron kolin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka kan yakar annobar, inda baki daya shugabannin suka yanke shawarar karfafa hadin gwiwa da juna da daukar matakai na bai daya a yaki da cutar. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma tura rukunonin likitoci da jami’an lafiya zuwa kasashen Afirka, tare da samar da gudummawar kayayyakin yaki da cutar ga kusan kowace kasa a Afirka da ke da bukatar hakan. Domin kiyaye zaman lafiya da tsaro a Afirka, kasar Sin ta kuma samar da gudummawar aikin soja ga tarayyar Afirka da kuma rundunar hadin kan kasashe biyar na yankin Sahel, tare kuma da tura jami’an kiyaye zaman lafiya don su shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke aiwatarwa a kasashen Afirka. A halin yanzu, kimanin sojojin kasar Sin 2100 ne suke aiwatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya shida na MDD a kasashen Afirka. Domin sa kaimin ci gaban kasashen Afirka, Sin ta hada gwiwa da kasashen Afirka wajen tsara shirye-shiryen hadin gwiwa goma da matakai takwas da za a dauka tare da aiwatar da su, inda ta ba da taimako wajen gina layukan dogon da suka kai sama da kilomita 6000 da kuma hanyoyin mota da tsawonsu ya kai kilomita 6000, baya ga kuma tashoshin jiragen ruwa kusa 20. Ban da haka, ta kuma aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ta fannonin samar da ci gaban zamani da suka hada da tattalin arziki ta yanar gizo da rayuwar birane ta zamani da makamashi mai tsabta da kuma fasahar sadarwar 5G.

Karkashin tsarin MDD, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan al’ummar kasashen Afirka wajen rungumar zaman lafiya, tare da taimaka musu wajen raya kasashensu na zamani. Baya ga haka, za ta kuma ci gaba da kare moriyarsu a dandalin kasa da kasa. Daidai kamar yadda Mr. Wang Yi ya bayyana, Sin na son tafiya kafada da kafada da kasashen Afirka, don tabbatar da kyakkyawar makomar bai daya a tsakanin sassan biyu. (Lubabatu)