logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin ganin an raba alluran rigakafin COVID-19 cikin adalci

2020-12-04 19:40:16 CRI

Kasar Sin na kokarin ganin an raba alluran rigakafin COVID-19 cikin adalci

Ya zuwa yanzu, mutanen da suka rasu sakamakon COVID-19 ya wuce miliyan 1.5 a duniya, kuma har yanzu cutar ta yaduwa. Bisa wannan hali da ake ciki, allurar rigakafi ta zama kalmar da kowa ke ambata.

A ranar 2 ga watan Disamba, kasar Burtaniya ta amince da amfani da sabbin alluran rigakafin kamfanin Pfizer na kasar Amurka da na kamfanin BioNTech na kasar Jamus.

A Amurka, sabbin muhimman takardun da kafar yada labarai ta CNN ta samu na nuna cewa, za a gabatar da rukunin farko na sabbin rigakafi da kamfanin Pfizer ya hada a ranar 15 ga Disamba, sannan kuma za a gabatar da rukunin farko na rigakafin na kamfanin Moderna a ranar 22 ga Disamba.

A nata bangare, kasar Sin ta jaddada cewa, a shirye take ta samar da alluran rigakafi masu yawa.

Kwanan baya, bayan da mataimakiyar firaministar kasar Sun Chunlan ta duba yadda wasu kamfanonin kasar ke aikin nazari da samar da alluran rigakafi ta nuna cewa, yanzu haka 5 daga cikin alluran rigakafi 14 na kasar, sun shiga mataki na uku na gwaji bisa ka’idoji da matsayin da aka gindaya.

Bisa ci gaban da ake ta samu wajen nazari da samar da alluran rigakafin na COVID-19, yadda za a rarraba alluran rigakafin a fadin duniya na kara jan hankali sosai. Yadda za a sanya alluran rigakafin su kasance kayayyakin da kowa da kowa daga ko wace kasa za su iya amfana da su har ma su iya samu, ta kasance matsalar gaggawa da duniya ke fuskanta.

Kasar Sin ta sha nanata tabbatar da ganin cewa, suma kasashe masu tasowa sun iya samun alluran da suka dace, masu inganci da kuma amfani.  

A yayin da yake halartar taron musamman na yaki da cutar COVID-19 da MDD ta shirya ta bidiyo a ranar 3 ga wata, wakilin musamman na shugaban kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya kara jaddada cewa, kasarsa na tsayawa kan matsayin alluran rigakafi na zama kayayyakin jama’ar duniya, kuma tana kokarin ba da tabbaci wajen samar da isassun alluran rigakafi masu araha ga kasashe masu tasowa. Ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin na gaggauta gwaji na uku na alluran rigakafi, bayan da aka gama ayyukan nazari da samarwa da soma amfani da su, za ta samar da su ga kasashe masu tasowa, don ba ta gudummawa wajen kafa kyakkyawar makoma mai kyau a fannin kiwon lafiya ga daukacin dan Adam.

Ra’ayi mai yakini da kasar Sin ta nuna da aikatawa a zahiri kan batun alluran rigakafi, sun jawo hankula da tabbacin kasashen duniya

Wasu manazarta sun nuna cewa, farashin alluran rigakafin na kasar Sin ba shi da tsada don haka, ko shakka babu sun fi jawo hankulan kasashe masu tasowa. Baya ga haka, matakan da kasar Sin ta dauka sun nuna matsayinta na babbar kasa dake sauke nauyin dake kanta, wadda kuma ke kokarin cika alkawarin da ta yi. (Bilkisu Xin)