logo

HAUSA

Sin ta yi nasarar tashi saman na’urar bincike a waje da doron duniya

2020-12-04 13:42:39 CRI

Sin ta yi nasarar tashi saman na’urar bincike a waje da doron duniya

A jiya Alhamis 3 ga wata, da misalin karfe 23 da minti 10, na’urar injin ta sashen tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5 ta yi aiki har tsawon mintoci shida, daga baya ta yi nasarar harba sashen tashi sama wanda ke dauke da samfuran da ta tattara zuwa falakinsa na kewayen duniyar wata, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta cimma burin tashi saman na’urar bincike a waje da doron duniya.

Kamar yadda aka sani, akwai matukar wahala sashen tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5 ya tashi sama a gefen duniyar wata, saboda babu cikakken tsarin harba na’ura a wajen, wato ba zai yiyu a harba na’urar a gefen duniyar wata kamar yadda aka yi a gefen doron duniya ba, shi ya sa ana yin amfani da sashen sauka na na’urar yayin da ake harba na’urar tashi sama, kuma kila ne sashen tashi sama na na’urar zai gamu da wahala yayin tashin sama sakamakon matsaloli iri daban daban da zai gamu da su, alal misali, rashin tabbacin siffarsa ta tashin sama, da kayyadadden gudanarwar aikin na’urar injin, da bambancin muhalli tsakanin doron duniyarmu da duniyar wata da sauransu, kana babu tsarin shawagin tauraron dan Adam a duniyar wata, a don haka sashen tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5 yana bukatar taimakon na’urorin tantancewa dake aiki a doron duniya ta hanyar yin amfani da na’urar musamman dake jikinsa, domin shiga falakin kewayen duniyar wata da aka tsara bisa siffar da ta dace.

Mataimakin darektan kula da aikin tsara na’urar bincike ta Chang’e-5 dake aiki a cibiya ta biyar ta rukunin kimiyya da fasaha na zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin Xing Zhuoyi ya yi mana bayani cewa, “Mun yi kidaya, idan an kara nauyin sashen tashi sama da kilo daya, to ana bukatar kara nauyin na’urar binciken da kusan kilo hudu, ana iya cewa, nauyin sashen tashi sama yana da matukar muhimmanci, a gaskiya mun sha wahala yayin da muka tsara na’urar, saboda dole ne mu tabbatar cewa, sashen tashi sama na na’urar binciken zai tashi sama a gefen duniyar wata cikin nasara.”

A ganin mai tsara tsarin alkalumai na na’urar bincike ta Chang’e-5 dake aiki a cibiya ta biyar ta rukunin kimiyya da fasaha na zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin Cheng Xiahui, yayin da ake gudanar da aikin harba sashen tashi sama na na’urar, dakika ta farko ta aikin ta fi muhimmanci, tana mai cewa, “Hakika a farkon aikin harba sashen tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5, ba zai yiwu mu sarrafa sashen ba, sai dai na’urar injin tana sarrafa shi kawai, bayan dakika ta farko, na’urar shiga falaki za ta karbe sashen, daga baya zai tashi sama bisa shawagin da aka tsara, shi ya sa mun damu sosai, saboda akwai wuya matuka na’urar shiga falaki ta karbi sashen tashi sama.”

Abun faranta rai shi ne, kafin sashen ya tashi sama, sashen sauka da sashen tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5 sun bude tutar kasar Sin a gefen duniyar wata, daga baya sun rabu, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta nuna tutarta da ita kanta kasa daya kacal a gefen duniyar wata.

Game da aikin na’urar bincike ta Chang’e-5 a nan gaba, mataimakin shugaban sashen kula da mataki na uku na cibiyar binciken duniyar wata da aikin zirga-zirgar sararin samaniya ta hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin Wang Qiong ya bayyana cewa, “Nan gaba wato bayan sashen tashi sama na na’urar binciken ya tashi sama, za a gyara falakinsa har sau hudu, domin cimma burin hada sashen da sashen falaki da kuma sashen komawa, daga baya za mu fara gudanar da sabon mataki na aikinmu wato za a hada su waje guda a cikin kwanaki uku masu zuwa.”

Bayan sassan uku sun hadu, za a mika samfuran da aka tattara a gefen duniyar wata cikin sashen komawa, domin dawowa nan doron duniya.

Yanzu haka na’urar bincike ta Chang’e-5 tana kan hanyarta ta dawowa, babban mai tsara na’urar dake aiki a cibiyar sarrafa zirga-zirgar sararin samaniya ta birnin Beijing Xie Jianfeng ya bayyana cewa, “Tun farkon da aka harba na’urar, har zuwa yanzu, ana iya cewa, ana gudanar da ayyuka bisa matakan da aka tsara lami lafiya, ana sa ran zata dawo nan doron duniyarmu cikin lumana.”(Jamila)