logo

HAUSA

Dalibar dalke sayar da furanni a cikin makarantar, don tattara kudin samun jinya ga mahaifiya

2020-12-03 08:52:12 CRI

Zhang Xiaowen ‘yar asalin lardin Henan na kasar Sin, wadda take da shekaru 23, daliba ce a wata kwaleji. Zhang Xiaowen ta yi fama da mummunar cutar melanoma a shekarar 2013. Yayin da take fama da cutar, an gano cewa mahaifiyarta na dauke da cutar sankarar huhu a shekarar 2019. A karkashin matsin lamba daga iyali da karatu, Zhang Xiaowen ta fara sayar da furanni a cikin makarantarsu, don tattara kudin samun jinya ga mahaifiyarta. Ta wallafa a dandalin sada zumunci game da yadda take fama da cutar sankara a cikin shekaru 7, tana mai bayyana burin ta na “zama lafiyayyar yarinya”. Tana fatan mutane masu himma za su ba da taimako, don ba ta, da iyalinta kwarin gwiwar ci gaba da rayuwa. (Bilkisu)