logo

HAUSA

Na’urar bincike ta Chang’e-5 tana tattara samfura a gefen duniyar wata

2020-12-03 12:19:51 CRI

Na’urar bincike ta Chang’e-5 tana tattara samfura a gefen duniyar wata

A safiyar jiya Laraba 2 ga watan Disamba da misalin karfe hudu da minti 53, sashen kula da sauka da tashi sama na na’urar bincike ta Chang’e-5 sun hada kuma sun fara hakowa samfura a gefen duniyar wata bisa shirin da aka tsara.

A yammacin ranar 1 ga wata, na’urar bincike ta Chang’e-5 ta sauka a gefen duniyar wata cikin nasara, daga baya ta fara tattara samfura a cikin kwanaki biyu masu zuwa, yanzu haka na’urar tana daukar samfura a wurare daban daban dake gefen duniyar wata ta hanyoyi biyu wato hakowa samfura da na’urar haka, da kuma karbar samfura kai tsaye daga gefen duniyar wata, gaba daya za ta dauko tabon duniyar wata da nauyinsu zai kai kilo biyu domin dawo da su doron duniyarmu.

Mataimakin shugaban sashen kula da mataki na uku na cibiyar binciken duniyar wata da aikin zirga-zirgar sararin samaniya ta hukumar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin Wang Qiong ya bayyana cewa, “Da farko, na’urar bincike ta Chang’e ta haka samfura a gefen duniyar wata, daga baya ta ajiye samfuran a cikin akwatin da muka shirya a cikin sashen tashi sama na na’urar, bayan na’urar binciken ta kammala daukacin ayyukan dauko samfura, za ta ajiye su cikin akwatin, kuma za ta rufe akwatin.”

Wang Qiong ya ci gaba da cewa, na’urar binciken za ta dinga karbar samfuran a gefen duniyar wata har tsawon awoyi sama da ashirin, lokacin da ya fi aikin haka samfura yawa, yana mai cewa, “Dalilin da ya sa haka shi ne, mun tsara shirin haka samfura a gefen duniyar wata, wato muddin na’urar haka ta kai zurfin da muka tsara bisa shiri, to shi ke nan ta kammala aikinta, amma yayin da na’urar take gudanar da aikin karbar samfura a gefen duniyar wata, tana bukatar karin lokaci saboda mun zabi wurare sama da goma bisa hakikanin yanayin da ake ciki, a don haka na’urar binciken za ta gudanar da aikin karbar samfura sau da dama.”

Hakika akwai babbar wahala ga na’urar bincike ta Chang’e ta gudanar da aikin haka tabon duniyar wata, ya zama wajibi ta dauko samfuran tabo masu amfanin yin nazari, saboda za a yi amfani da su wajen yin nazari kan asalin duniyar wata da sauye-sauyenta, mataimakin babban mai tsara na’urar bincike ta Chang'e-5 wanda ke aiki a rukunin kimiyya da fasaha na zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin Peng Jing ya yi nuni da cewa, “Idan an yi amfani da hanya daya tilo yayin da ake karbar samfura a gefen duniyar wata, wata kila irin samfura ko yawan samfura ko nauyin samfura ba za su iya biyan bukatar aikin nazarinmu ba, yanzu haka na’urar binciken tana gudanar da aikinta ta hanyoyi biyu wato haka samfura da na’urar haka, da kuma karbi samfura kai tsaye daga gefen duniyar wata, lamarin da zai cimma burinmu na samun karin samfura iri daban daban, kana kamar yadda aka sani, ba zai yiwu ba a gyara na’urar binciken bayan da aka harbe ta zuwa sararin samaniya, shi ya sa muna da damar daukar samfuri daya ne kacal, dole ne mu tsara shirin gudanar da aikin haka samfura ta hanyoyi guda biyu, alal misali, idan na’urar binciken ta gamu da matsala, ko kuma ta lalace, muna iya daukar mataki na daban domin tabbatar da cewa, na’urar binciken za ta kammala aikinta cikin nasara, wato idan na’urar binciken ta kasa daukar samfura ta hanyar haka, to za ta yi nasarar karbar samfura ta hanyar karbar samfura kai tsaye daga gefen duniyar wata.”

An lura cewa, bayan da na’urar bincike ta Chang’e ta kammala aikin dauko samfura a gefen duniyar wata, kuma ta kammala aikin adana su cikin akwatin da aka shirya, sai dai za ta dawo doron duniyarmu nan take, wato za ta sauka a yankin Siziwang na jihar Mongolia ta gida dake arewa maso yammacin kasar Sin.(Jamila)

jamila