logo

HAUSA

Diego Maradona ya rasu yana da shekaru 60

2020-12-03 10:03:20 CRI

Diego Maradona ya rasu yana da shekaru 60

Diego Maradona, shahararren dan kwallon kafa ne da ya jagoranci kungiyar kasar sa Argentina wajen lashe kofin duniya na shekarar 1986, kuma labarin rasuwar sa ya karade sassan duniya a Larabar makon jiya. Rahotanni sun tabbatar da cewa, bugun zuciya ne ya yi sanadiyyar rasuwar tsohon dan wasan.

Mai Magana da yawun Maradona Sebastian Sanchi, ya ce tsohon dan wasan ya rasu ne a gidan sa dake Tigre, a arewacin birnin Buenos Aires fadar mulkin Argentina, lokacin da yake farfadowa daga tiyata da aka yi masa a kwakwalwa cikin karshen watan da ya gabata.

Larabin rasuwar wannan gwarzo ta ja hankalin masoyansa wadanda suka shiga yanayi na alhini, baya ga ita kan ta gwamnatin Argentina da ta ayyana zaman makoki na kwanaki 3, domin juyayin wannan babban rashi.

Cikin wani sakon nuna alhini da ya wallafa a shafin sa na Tiwita, shugaba Alberto Fernandez ya ce "Ka kai mu mafi daukakar matsayi a duniya, Ka kuma sanya mu matukar farin ciki. Kai ne mafi kwarewar su. Mun gode da ka kasance tare da mu Diego. Za mu yi kewar rashin ka duk tsawon rayuwar mu” .

" Maradona ya fara haskawa a fannin tamaula ne lokacin da ya bugawa karamar kungiyar Argentinos kwallo a watan Oktoba na shekarar 1976, kwanaki 10 kafin ya cika shekaru 16 da haihuwa. Ya kuma yi fitar farko ga kungiyar kasar sa a babban wasa da ta buga watanni 4 bayan hakan, ko da yake kocin kungiyar a wancan lokacin Cesar Luis Menotti, bai ba shi damar bugawa babbar tawagar kasar wasannin cin kofin duniya na shekarar 1978 ba, yana mai cewa dan wasan bai shirya ba.

Ba da jimawa ba dan wasan gaba Maradona, ya nunawa duniya irin baiwar da yake da ita a fannin buga kwallo, da iya wasa da ita, da sarrafa ta tsakanin sauran ‘yan wasa.

Bayan shafe shekaru sama da hudu a kungiyar Argentinos Juniors, Maradona ya koma kulaf din Boca Juniors, inda ya ci kwallaye 28 a wasanni 40, wanda hakan ya ba shi damar sauyin sheka ta kudi har dalar Amurka miliyan 8, sauyin sheka mafi tsada da wani dan wasa ya taba samu a lokaci.

To sai dai kuma, lokacin da ya shafe a kungiyar birnin Catalan cike yake da matsaloli, duba da yadda ya sha fama da cutar hanta ta hepatitis. Bayan cin kwallaye 38 a wasanni 58, Maradona ya bar Blaugrana zuwa Napoli, inda a wannan lokacin ma ya sake kafa tarihin sauyin sheka ta dalar Amurka miliyan 10.5 a watan Yulin shekarar 1984.

A gasar Serie A kuwa, Maradona ya kara haskawa, a matakin kungiyar, da ma wasanni da ya buga na kasa da kasa ga Argentina.

Kasa da shekaru 2 da zuwan sa Italiya, ya taimakawa Argentina lashe kofin duniya na shekarar 1986 a Mexico. Kusan wannan ne ma lokaci mafi daukaka da ya samu a tarihin kwallon sa, a wannan gasar ne ya ci kwallo da hannu, kwallon da aka rika yi mata kirari na bajimta. Kwallon da ya ja hankali ya jefa ta a zare ne yayin wasan Argentina da Ingila a wasan kusa da kusa da na karshe.

Mintuna 4 bayan hakan ne kuma ya sake zarar kwallo yayi gudun da ya haura nisan rabin filin wasan na Azteca, tare da yanke masu tsaron baya 4, ya kuma jefa kwallo a ragar mai tsaron gida Peter Shilton, a wata kallo da ake ganin ta kafa tarihi a kwallaye mafiya kayatarwa a wannan karni.

A Italiya, Maradona ya jagoranci Napoli zuwa lashen kofin Serie A na farko a tarihin ta a kakar wasa ta 1986 zuwa 1987. Kaza lika kungiyar ta lashe Coppa Italia a 1987, da kafin UEFA na 1989, da wani kofin na Serie A a kakar 1989 zuwa 1990.

To sai dai kuma, Maradona ya gamu da cikas a fannin rayuwa, inda ya yi ta fama da matsalolin shaye shayen kwayoyi da barasa.

A shekarar 1991, an dakatar da shi buga wasa har tsawon watanni 15, bayan gano yana amfani da kwayoyin kara kuzari, a wannan lokaci ne kuma batun ta’ammali da horas Iblis ya fito fili duniya ta sani.

Maradona ya bar kungiyar Napoli shekara 1 bayan shiga wannan matsala, inda ya koma Sevilla, sai dai ya kasa komawa ganiya cikin watanni 12 da ya yi kungiyar ta Sifaniya. Daga nan ne kuma ya koma Argentina a shekarar 1993 don taka leda a kungiyar Newell's Old Boys, kafin ya bayyana rataye takalman sa lokacin da yake bugawa Boca Juniors wasa, kungiyar da ya bugawa wasanni 30 kacal, cikin su kuma ya ci kwallaye 7 a tsawon kaka biyu.

Duk da koma bayan da ya gamu da shi cikin wadannan shekaru 4, Maradona ya taimakawa kungiyar kasar sa kaiwa ga wasan karshe na cin kofin duniya da aka buga a Italiya, inda suka yi rashin nasara a hannun Jamus ta yamma a wasan karshe. Wannan wasa dai shi ne kusan karon karshe da Maradona ya taimawa babbar kungiyar Argentina a matsayin sa na dan wasa.

Ya kammala buga wasa ga kungiyar kasar sa lokacin da aka sallame shi daga gasar cin kofin duniya na gaba, wato wanda aka buga a Amurka, sakamakon gwajin da ya nuna cewa ya sha abubuwa masu kara kuzari.

Maradona ya koma aikin horas da ‘yan wasa bayan ya ajiye takalma. A shekarar 2008 ne kuma aka nada shi babban kocin Argentina, kafin a karbe wannan aiki daga hannun sa kasa da shekaru 2 da jagorantar kungiyar, bayan da Argentina ta yi rashin nasara hannun Jamus da ci 4 da nema, a wasan kusa da kusan na karshe a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010 da aka buga a Afirka ta kudu.

Daga baya, Maradona ya sha fama da nau’oin rashin lafiya. A shekarar 2004, an kwantar da shi a asibiti, sakamakon matsalar zuciya da numfashi masu nasaba da shan kwayoyi. An kuma yi masa tiyata har karo 2 don magance nauyin jiki da ya samu, sakamakon yawan shan barasa.

A shekarar 2019, an sake yiwa Maradona tiyata domin dakatar da jini da ya balle a cikin sa, kana an masa wata tiyatar a gwiwa.

A ranar 2 ga watan Nuwambar bana, kwanaki 3 bayan cikar sa shekaru 60 da haihuwa, an kara kwantar da shi a asibiti. Bayan gwaje gwaje an gano yana da wani ciwo a kwakwalwa, kana likitoci sun masa aikin gaggawa washe gari. An kuma sallame shi daga asibiti a ranar 11 ga watan na Nuwamba, kafin rai yayi halin sa yana tare da babbar ‘yar sa.

A dai wannan gaba da ake alhinin rasuwar wannan tauraron dan kwallo, manyan ‘yan wasa, da masu ruwa da tsaki a fannin tamaula na ta mika sakon ta’aziyyar su.

Franco Baresi ya ce: "Maradona ya wahalar da mu, ya ci mu tarin kwallaye, wani lokacin za ka ture shi, yana jin zafi amma ba ya korafi. Yana da bin ka’idar wasa. Dukkanin abokan wasan sa suna kaunar sa, Baya barin matsayin sa ya dakatar da shi, baya barin mutane su dakatar da shi, musamman masu zuwa kallo domin ganin kwarewar sa."

Eric Cantona ya ce: "Zan yi kewar Diego a wuri na ba ka mutu ba. Bani da Kalmar bayyana yadda nake ji da rasuwar ka."

Jurgen Klopp ya ce: "Shekaru na 53, duk tsawon rayuwa ta, ina tare da shi. Diego dan wasa ne mai burge kowa. Maradona ka yi fama da matsaloli. Zan yi matukar kewar ka."

Gary Lineker ya ce: "Kusan ana iya cewa dan wasa ne mafi kwarewa a duk wannan karni, ko ma ace wanda ba a taba yin kamar sa ba. Bayan shafe rayuwar nasara da kalubale, ina masa fatan samun hutu bayan mutuwa."

Sachin Tendulkar ya ce: "Kwallon kafa da ma duniya baki daya sun yi rashin babban tauraro. Fatan za ka huta Diego Maradona! Tabbas za mu yi kewar ka."

Lionel Messi na cewa: Ya bar mu amma yana nan, saboda Diego zai wanzu a zukatan mu. Zan ci gaba da tunawa da kasancewar mu tare da kai, zan kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta’aziyya ta ga ‘yan uwa da iyalin ka. Fatan ka huta."

Cristiano Ronaldo ya ce: "Tauraron da ba a yi kamar sa ba, dan wasa mai sihirin kwallo. Ka bar mu da wuri amma ka bar tarihi, da gibin da ba za a iya cike shi ba. Fatan ka huta. Ba za a taba mantawa da kai ba."

Pele ya ce: "Akwai abubuwan fada da yawa, amma a yanzu, fata na shi ne ubangiji ya karfafi iyalan ka kan juriyar rashin ka. Wata rana, ina fatan za mu sake yin wasa tare can a sama."

Gabriel Batistuta ya ce: "Muna matukar godiya, ina kuka don rashin ka. Ina tare da iyalin ka. Fatan ka huta, aboki na Diego."

Ronaldinho ya ce: "Fatan hakuri ga iyalan ka, da ma dukkanin sauran masu kaunar wannan gwarzo. Aboki na, abun koyi na, lamba 10 na, na gode maka bisa kasancewa ta tare da kai, a wajen lokacin walima ko wurin shakatawa. Fatan ka huta, abun koyi na, Ina kaunar ka."

Rivaldo ya ce: "Mun kaunaci juna mun farantawa juna, ba zan taba mantawa ba. Kai mutum ne mai ban sha’awa, mai babbar zuciya. Allah ya jibinci zukatan iyalan ka, da masoya kwallon kafa, da ma daukacin al’ummar Argentina.