logo

HAUSA

Tattalin arzikin zamani ya zama sabon tubali ga tattalin arzikin bunkasa kasar Sin

2020-12-02 09:06:05 CRI

Tun bayan da annobar COVID-19 ta bulla a farkon wannan shekara, kasashen duniya ke ci gaba da fuskantar matsaloli iri daban daban kama daga durkushewar tattalin arziki, hasarar guraben ayyukan yi, baranazar fannin kiwon lafiya da makamantansu. Koda yake, kowace kasa tana ci gaba da daukar matakan daidaita matsalolin da take fama da su. A kasar Sin, tun a shekarun baya bayan nan, gwamnatin kasar ta himmatu wajen daukar kwararan matakan kyautata matsayin tattalin arzikinta, da bunkasa kasuwannin cikin gida domin biyan muradun al’ummarta, a hannu guda kuma tana kara bude kofarta ga ketare domin cudanyar tattalin arziki da cinikayya da kasa da kasa. Cibiyar nazarin fasahar intanet ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa, tattalin arzikin zamani na kasar ya kai yuan triliyan 35.8, kwatankwacin dala triliyan 5.45 a shekarar 2019, wanda ya kai kashi 36.2 bisa 100 na yawan GDPn kasar. 

Tattalin arzikin zamani ya zama sabon tubali ga tattalin arzikin bunkasa kasar Sin

Rahoton ya nuna cewa, barkewar annobar COVID-19 ta kara fito da muhimmancin intanet a fili, yayin da tattalin arzikin zamani ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi wajen rage tasirin illar annobar, fannin ya daidaita yanayin tattalin arziki da kuma inganta tsarin tafiyar da shugabanci a matakin kasa da kasa.

Ya zuwa karshen watan Mayun bana, kamfanin yanar gizo na fiber-optic na kasar Sin yayi nasarar hadewa dukkan yankunan biranen kasar da na karkara, inda aka samu masu mu’amala da kamfanin na fiber-optic sun kai kashi 93.1 bisa 100 na yawan adadin masu amfani da hanyoyin intanet a duk kasar, wanda shine adadi mafi girma a duniya, a cewar rahoton.

Tattalin arzikin zamani ya zama sabon tubali ga tattalin arzikin bunkasa kasar Sin

Haka zalika, a shekarar 2019, akwai tashoshin fasahar 4G miliyan 5.44 a kasar Sin, kuma adadin datar da masu wayoyin hannu ke amfani dashi ya kai biliyan 122, wanda shine adadin mafi yawa a duniya. Ya zuwa watan Satumbar wannan shekarar, kasar Sin ta gina tashoshin fasahar 5G sama da 480,000. Kana hada hadar ciniki na zamani na kasar Sin ya kai yuan triliyan 34.81 a bara, inda aka samu karin kashi 6.7 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2018.

Bisa kididdigar da hukumar kula da aika wasiku da kayayyaki ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa ranar 16 ga watan Nuwambar bana, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a kasar Sin ya zarce biliyan 70, wanda ya fi na shekarar bara. An samu babban ci gaba a fannin aika kayayyaki a kasar ne sakamakon bunkasuwar ciniki ta yanar gizo a duk fadin kasar. (Ahmad/ Ibrahim/Sanusi)