logo

HAUSA

Yaushe Amurka Za Ta Daina Zargi Marasa Tushe Kan Kasar Sin?

2020-12-02 17:48:18 CRI

Yaushe Amurka Za Ta Daina Zargi Marasa Tushe Kan Kasar Sin?

Makiyinka idan ka yi tafiya a ruwa ma, zai ce ka tayar da kura. Duk wani abu mai kyau da kasar Sin ta yi, Amurka na kallonsa a matsayin maras kyau. Wannan ba shi ne karon farko da Amurka ke neman bata sunan kasar Sin ko kamfanoninta ba tare da gabatar da kwararan shaidu ba.

A baya kasar Amurka ta sha tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar, kamar batun yankin musamman na Hong Kong, da yankin Taiwan, da yankin Xinjiang da sauransu babu gaira babu dalili. Inda take fakewa ko dai da batun Demokiradiya ko ’yancin bin addini ko kare hakkin bil-Adama da makamantansu, wadanda dukkansu Amurkar ke fakewa da su, don neman shiga shoro ba Shanu.

Amma duk da shaidu da muhimman takardun bayanai da kasar Sin ta gabatarwa duniya, don karyata zargin da Amurka ke yi kan harkokin cikin gidan kasarta, bangaren na Amurka bai daddara ba. Abin ka da wanda ya yi nisa, aka ce ba ya jin kira.

A kwanakin baya ma, sakataren sojojin ruwan Amurka da kwamandan sojojin saman Amurka dake yankin Fasifik, sun furta wasu kalaman da ba su dace ba game da kasar Sin. Amma a martanin ta kasar Sin ta ce “Wannan wani tsohon yanayi ne da wasu Amurkawa ke bi, kuma wani salo ne na ra’ayin cacar baka, da ra’ayi na kashin kai, kuma kasar Sin tana adawa da su.

Masana na ganin cewa, irin wannan mataki na Amurka, ya saba ka’idojin hadin gwiwar kasa da kasa, baya ga yiwa muradu da martabar kasar Sin illa a idon duniya.

Wannan ba komai ba ne illa kishin ci gaban da kasar Sin ta samu, sai dai wannan ba zai girgiza aniyyar kasar Sin ta samun ci gaba cikin lumana ba.

Sanin kowa ne cewa, har kullum kasar Sin, tana martaba dokoki da ka’idojin hadin gwiwa na kasa da kasa daga dukkan fannoni. A don haka ya kamata Amurka ta bude idonta game da abubuwan dake faruwa a duniya, ta kuma kalli kasar Sin ba tare da nuna son kai ba, ta kuma tafi da zamani tare da kara taka rawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya, sannan ta mayar da hankali kan kalubale da tarin matsalolin dake damunta, tun kafin wankin hula ya kai ta dare. (Ibrahim Yaya)