logo

HAUSA

Gan Youqin dake taka muhimmiyar rawarsu, wajan kawar da talauci

2020-12-02 16:29:30 CRI

A cikin kasar Sin dake samun saurin ci gaba a fannin tattalin arziki na “taurari a kafar intanet”, shirin kai tsaye na sayar da kayayyaki ya kasance wata alamar zamani, wadda ke samun karbuwa sosai a nan kasar. Irin alamar dake amfani da dandalin sada zumunta na yanar gizo don tattara dumbin masu sha’awar “taurarin intanet”, tare kuma da canza tasirin masu sha'awar zuwa fa'idodin tattalin arziki, shi ne abin alajabi na zaman al’ummar kasar a yanzu haka.

Bisa wannan yanayin da ake ciki, "taurarin intanet" na taka muhimmiyar rawarsu, wajan kawar da talauci, da raya al’umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni.  Gan Youqin na daya daga cikinsu.  

Gan Youqin dake taka muhimmiyar rawarsu, wajan kawar da talauci

Gan Youqin cikin gama garin kauyawa dake fama da talauci, a kauyen Suwutang dake garin Sanhai na gundumar Lingshan, ta lardin Guangxi dake kudancin kasar Sin. Tun daga watan Mayu na shekarar 2017, ta soma shahara ta hanyar kirkirar bidiyo a manhajoji. Daga baya kuma, ta yi amfani da hanyar daukar gajerun bidiyo, da watsa shirye-shirye kai tsaye don tafiyar da tallar kayayyakin amfanin gona na garinsu. Bisa kididdigar da aka yi, a cikin shekarar 2019, Gan Youqin ta taimaka wa garinsa wajen sayar da kayayyakin amfanin gona, har kilo miliyan 6, jimilar kudin da aka samu a fannin ta wuce RMB yuan miliyan 30.

"Kawai na dauki hoto ne game da rayuwata. Ban taba tunanin zama taurariyar intanet ba, balle ma in zama ‘yar kasuwa dake amfani da hanyar intanet, har ma da haifarwa mazauna kauyenmu yanayi na samun wadata." Wadannan kalaman Gan Youqin ne, wadanda ke da sauki, kuma gaskiya ta fada.

Gan Youqin, mai shekara 40 a wannan shekara, wadda da ma ta taba aiki a waje, amma a shekarar 2002 ta koma garinsu domin yin aikin gona a saboda ‘ya’yanta.

"Ina tashi cikin duhun kowace safiya, in je gona da safe, kuma in tafi gida don dafa abinci da tsaftace gida da daddare, da kula da yara da tsofaffi a gida." A wancan lokacin, Gan Youqin ba ta yi tsammanin cewa za ta sake samun wata dama a rayuwarta ba.

Bayan shekaru 15, wata dama ta zo ba zato ba tsammani. A watan Mayu na shekarar 2017, dan dan uwanta, wanda ya kammala karatunsa a jami’ar kudi da tattalin arziki ta fannin ilmin fina-finai da talabijin, ya zabi komawa gida don fara kasuwanci. A wancan lokacin, yana kokarin daukar wasu kananan bidiyo na karkara, da kuma sanya su a Intanet. A cikin wasu dan lokuta, ya kasa samun jarumar da za ta dace, don haka ya ba da shawara ga Gan Youqin, wadda take son yin abinci, don yin gwaji.

Bidiyo na farko da suka yi shi ne nuna yadda ake hada kwan da aka sanyawa kayan zaki da nama. Saboda wannan ne karo na farko da take fuskantar kyamara, Gan Youqin ta firgita sosai. Ta ce, "Muddin ana nuna kyamara a fuskata, ba zan iya yin magana ba." A karshe dai, an yi amfani da duk yammacin ranar don daukar wannan bidiyo na tsawon minti 5.

Gan Youqin dake taka muhimmiyar rawarsu, wajan kawar da talauci

Amma, ba zato ba tsammani, bidiyon ya shahara sosai tsakanin masu amfani da yanar gizo. "A cikin 'yan kwanaki kadan, sama da mutane 200,000 sun kalla, fiye da dukkan mutanen garinmu." Wannan ya ba Gan Youqin mamaki sosai.

Bayan nasarar farko da ta cimma, Gan Youqin ta fara yin gajeren bidiyo game da abinci bisa shawarar dan dan uwanta da mijinta. Bidiyon abincin nata ya ja hankali sosai. Daga baya, dan dan uwana ya kara ba ta shawarar ta sauya fasali, don haka suka yi kokarin fadadawa zuwa tsara bidiyo game da rayuwar karkara.

Daga baya, Gan Youqin da mijinta Lu Qisong sun soma aika tare, kuma su biyun sun yi amfani da gajerun bidiyo, don yin rikodin na aikinsu na yau da kullun a cikin filayen. Dafa abinci, yin aiki a filaye, jefa raga don kamun kifi, hawa bishiyoyi da dibar 'ya'yan itace ... wadannan abubuwa na yau da kullun, sun nadi bidiyo mai ban sha'awa sosai. Gan Youqin ta samu masu kallo a intanet masu yawa a cikin 'yan watanni kadan, ta hanyar nuna sabuwar rayuwar karkara mai ban sha'awa a cikin gajeren bidiyo.

To sai dai fa, akasin mutum sanannen a kafar Intanet, a kauyen su wasu sun rika yiwa Gan Youqin gani-gani.

Suna cewa "Me ya sa kullum wata mace dake karkara ke fita waje!" "Yaya abin yake ne, kullum tana daukar wannan da wancan da kyamara!" ...

Sukar da mazauna garin suka yi mata ya sa Gan Youqin ta zama mara taimako sosai, amma ra’ayinsu ya canza bayan da Gan Youqin ta soma aikin sayar da kaya a intanet.

A wancan lokacin, Gan Youqin ta kan sanya yadda take hawan dutse don sakawa bishiyoyi masu 'ya'yan itace taki, da dibar ' ya'yan itatuwa, da kuma dafa abinci da 'ya'yan itatuwa a Intanet. Sannu a hankali, wasu masu sha’awar aikin ta sun rika nuna goya baya ta hanyar saka sakwannin yabo a kasan bidiyon suna cewa: "' Ya'yan itatuwan gidanku suna da kyau, ko za ki iya sayar min da su? " An yi ta yin tambayoyi iri-iri wadannan, dana nan ne kuma sai Gan Youqin ta shirya bude wani shagon yanar gizo, don sayar da kayayyakin gargajiya na garinsu.....