logo

HAUSA

UNICEF: 2 bisa 3 na yaran ‘yan makaranta ba su da sadarwar intanet a gida

2020-12-02 11:41:26 CRI

Wani rahoto da asusun kula da kananan yara na MDD UNCEF ya wallafa da hadin gwiwar kungiyar sadarwa ta duniya, ya ce 2 bisa 3 na yara ‘yan makaranta ko yara biliayn 3 da ke tsakanin shekaru 3 zuwa 17, ba su da sadarwar intanet a gidajensu.

Rahoton mai taken “ Yara da matasa nawa ne suke da sadarwar intanet a gida?” ya kuma ce haka batun yake tsakanin matasa ‘yan shekaru 15 zuwa 24 wato kimanin miliyan 759 ko kaso 63 na matasa ba su da sadarwar intanet a gida.

Babbar Daraktar asusun UNICEF Henrietta Fore, ta ce yadda yara da matasa da dama ba su da sadarwar intanet ya wuce a kira shi da gibi a fannin sadarwar zamani, tana mai cewa, rashin intanet ba hana su damar shiga yanar gizo kadai yake yi ba, har ma da hana su damar gogayya a fannin tattalin arzikin zamani, inda ta ce yana nisanta su da duniya. Ta kara da cewa, yayin da aka rufe makarantu, kamar yadda aka yi saboda bullar COVID-19, lamarin na sanya su asarar karatu. Ta ce rashin sadarwar intanet na lahani ga makomar zuri’a ta gaba.

Baya ga haka, rahoton ya ce akwai gibi ta fuskar wurare a kasashe da ma yankuna. Wato kusan kaso 60 na yara ‘yan makaranta a duniya dake rayuwa a birane ba su da sadarwar intanet a gida, idan aka kwatanta da kusan 3 bisa 4 na takwarorinsu dake yankunan karkara. Rahoton ya ce matsalar ta fi shafar yaran yankin kudu da hamadar Sahara da na kudancin Asiya, inda ake samun yara 9 daga cikin 10 ba su da sadarwar intanet. (Fa’iza Mustapha)