logo

HAUSA

Na’urar bincike ta Chang’e-5 ta sauka a duniyar wata

2020-12-02 13:30:50 CRI

Na’urar bincike ta Chang’e-5 ta sauka a duniyar wata

A jiya da dare ne, na'urar binciken duniyar wata ta kasar Sin mai suna Chang'e-5, ta yi nasarar sauka a wurin da aka tsara a gaban duniyar wuta, daga nan ne kuma za ta fara aiki na tsawon kwanaki biyu a duniyar wata.

Da karfe 11 da minti 11 na daren ranar 1 ga watan Disamba, na’urar bincike ta Chang'e-5 ta yi nasarar sauka a yankin da aka riga aka tsara kusa da gaban wata da nisan digiri 51.8 a yammaci da nisan digiri 43.1 a kusurwar arewaci, kuma ya dawo da hoton saukarsa. Mataimakin daraktan cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta Beijing, He Jun ya bayyana cewa,

“Aikin saukar wannan na’ura yana da inganci sosai, wanda ke kafa harsashi mai karfi ga aikinmu na binciken duniyar wata da zai biyo baya, da kuma aikin dawowar na’urar doron kasa yadda ya kamata.”

An zabi yankin saukar da na’urar bincike ta Chang'e-5 ne a kusa da  tsaunukan Lumke a arewacin Oceanus Procellarum, wato tekun wata da ya fi girma a wata. Dalilin da ya sa aka zabi wannan yanki shi ne, masana kimiyya suna ganin cewa, ta fuskar yanayin kasa, za a iya samun dutsen irin na basalt a nan, idan aka kwatanta da yankunan da Amurka da Tarayyar Soviet suka zaba kafin saukar wata. Mataimakin babban mai ba da jagoranci na aikin binciken duniyar wata, kuma darektan cibiyar kula da aikin binciken wata da kumbuna karkashin hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, Liu Jizhong ya bayyana cewa,

“Lokacin da muke tsara yankin saukar, bai kamata kawai mu yi la'akari da yiwuwar aiwatar da aikin ba, amma kuma mu yi la'akari da ko zai ba da mahimmanci kan aikin nazarin kimiyya da za mu aiwatar. Ta fannin nazarin kimiyya, ya kasance wani sabon yanki ne saboda kasashen Amurka da Rasha ba su zabe shi ba, lokacin barkewar dutse mai aman wuta ya sha bamban da na yankunan da kasashen Amurka da Tarayyar Soviet suka dauko samfuran, don haka yana da ma’ana kwarai ta fuskar binciken kimiyya.”

Na’urar bincike ta Chang’e-5 ta sauka a duniyar wata

Game da muhimman abubuwa da wahalhalu na wannan aikin saukar na’urar din kuwa, mataimakin babban mai tsara na’urar bincike ta Chang'e-5, malam Peng Jing ya gabatar da cewa,

“Mun tsara yadda na’urar za ta kaucewa shingaye. A kusan tsayin mita 100 daga doron duniyar wata, za a yi amfani da kyamara don daukar hoton yankin kasa da na’urar da za ta sauka, daga baya za mu zabi wani wuri mafi dacewa a wannan yankin don soma aikin saukar. Wannan mataki na iya tabbata ne ko za a iya sauka kan wata daidai a karshe. Idan kafa daya ta na’urar ta sauka a rami, dayan kuma a kan dutse, to na’urar za ta karkata sosai. Idan mun yi aiki bisa wannan halin, to za mu fuskanci karin matsaloli a yayin da ake daukar samfura, da kuma tashi daga duniyar wata, don haka, matakin yana da muhimmanci kwarai da gaske.”

An ce, bayan kammala aikin saukar cikin nasara, na’urar dake daukar tauraron za ta fara aiki na kimanin kwanaki biyu a doron duniyar wata, don tattara samfuran wata. Mataimakin shugaban sashe na uku na cibiyar kula da aikin binciken wata da kumbuna na hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, Wang Qiong ya bayyana cewa,

“Bayan sauka a duniyar wata, za mu yi aiki kan yanayin farkon saman duniyar wata, daga baya za mu soma aiki da injuna masu dauke da nau’rori daban daban, da dauko amfura a saman wata da karkashin wata. Za a yi amfani da awoyi kimanin 20 don gudanar da aikin dauko samfura a duniyar wata, daga baya za a share fagen aikin tashi daga duniyar wata, bayan haka kuma, za a tabbatar da lokacin da ya dace don tashi daga doron wata.” (Bilkisu)