logo

HAUSA

Taron Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Bayyana Aniyar Kasar Sin Ta Kara Bude Kofa Ga Ketare

2020-12-01 20:58:02 CRI

Taron Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Bayyana Aniyar Kasar Sin Ta Kara Bude Kofa Ga Ketare

A yayin taron baje kolin kasar Sin da kungiyar ASEAN karo na 17 da aka rufe jiya Litinin, an gudanar da harkokin kara azama kan tattalin arziki da ciniki fiye da 150 ta yanar gizo da kuma a zahiri, an kuma daddale yarjejeniya kan shirye-shiryen hadin gwiwar zuba jari 86, wadanda yawan karuwar darajar shirye-shiryen ya kai matsayin koli a tarihi. Taron ya kara zurfafa huldar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kungiyar ta ASEAN da kuma mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki.

Ya kuma kasance wani mataki na daban da bangarorin 2 suka dauka wajen raya kyakkyawar makoma tare.

Taron na bana, ya sha bamban da tarukan da aka yi a baya. Yanzu ana yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wasu sassan duniya. Bude taron kamar yadda aka tsara, ya shaida cewa, kasar Sin tana dakile yaduwar annobar yadda ya kamata. Ta kuma bayyana aniyar kasar Sin ta kara bude kofarta ga ketare da kara azama kan hadin gwiwa a tsakanin ta da kungiyar ASEAN ta fuskar tattalin arziki da ciniki.

Hakika dai tun farkon wannan shekara, kasar Sin ta shirya wasu tarukan kasa da kasa a daidai lokacin da aka tsara. Kasar Sin tana himantuwa wajen samar wa ’yan kasuwa a gida da wajen kasar damar yin mu’amala da hadin gwiwa a ko da yaushe. Lamarin da ya bayyana aniyarta ta kara bude kofa ga ketare. Ba shakka kasar Sin wadda ke kara bude kofa ga ketare, tana kokarin farfado da kanta tare da duniya baki daya. Kasashen duniya, ciki had da kungiyar ta ASEAN za su ci gajiyar hakan. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan