logo

HAUSA

Labaran talakawa, sun bayyana jihar Xinjiang a matsayin mai haske

2020-12-01 12:38:13 CRI

Labaran talakawa, sun bayyana jihar Xinjiang a matsayin mai haske

A jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, talakawa suna gudanar da ayyukan da suke sha’awa, wadanda suka dace da rayuwar yau da kullum, kana kuma suke kyautata rayuwarsu. Lamarin da ya raya sana’o’i da hanyoyin samun kudin shiga a garesu. Jerin labaran mutanen, sun bayyana Xinjiang a matsayin wata sahihiyar jiha mai haske.

A shekarar da muke ciki, Lilia, ‘yar kabilar Rasha, ta samu wani aiki a kofar gidanta. A matsayin ta na ‘yar wurin, Lilia ta bude wani karamin shago a titin Liuxing dake birnin Yining na yankin Yili na kabilar Kazakh mai cin gashin kai, wanda ke sayar da wani abincin musamman, wato babban burodi irin na Rasha.

Bisa kanshin burodi, za a iya samun wannan shagon na Lilia dake cikin wani gini mai salon Rasha. Kasuwanci na bunkasa sosai a cikin shagonta. A cewar mazaunan wurin, yana da wuya ka samu burodin da kake so idan ka je da yamma.

Da take magana game da ainihin aniyar bude shagon, Lilia ta ce, tana matukar son cin irin babban burodin da kakarta take yi lokacin da take karama. Kuma bayan ta girma, sai ta fara sha’awar yada irin fasahar kakarta ta gasa babban burodin."

Titin Liuxing da shagon babban burodin na Lilia yake, sanannen yanki ne sakamakon kasancewarsa mai kusurwa shida. An gina shi ne a shekarar 1934. A cikin wannan unguwar da ke da fadin hekta 47, akwai mutanen kabilu da dama kamarsu kabilar Han, ta Uygur, ta Rasha, ta Kazakh, da kuma ta Hui dake zaune a nan.

Godiya ga aikin habakawa da gyaran titin tarihi da al'adu na Liuxing, wanda aka kaddamar a watan Satumban shekarar 2018, halin titin tana ta canzawa a kowace rana. Lilia, wacce ta rayu a nan tun kuruciya, tana da kyakkyawan fata game da ci gaban titin Liuxing a nan gaba, kuma ta yanke shawarar bude shagon sayar da babban burodi a wannan unguwa da ta sani.

A yanzu dai, titin Liuxing dake kiyaye daddaden abubuwa da tunani, ya zama titin kasuwanci na wasu mazauna wurin dake iya raya sana’o’insu a kofar gida. A halin yanzu, jimillar iyalai sama da 30 na titin Liuxing sun bude masaukin masu yawon bude ido, da gidajen shan kofi, da shagunan musamman, da dai sauransu a farfajiyarsu, lamarin da ya sa mazauna sama da 720 suka samun aikin yi a gida.

Shagon sayar da askirim mai sunan "Gulan Dam" da ya shahara a intanet wanda yake a farfajiyar kan titin Liguang yana daya daga cikinsu. Ma’anar Gulan Dam, ita ce furen kankara. Maigidan, Wang Cheng, shi ma dan yankin ne a Yining, a cewarsa, askirim din da aka yi da hannu a shagon yana amfani da kayan masarufi da fasahar gargajiya ta wurin. Yanzu shagon na iya sayar da askirim kusan 1,000 a kowace rana.

Tsohon dandano ake sayarwa, amma falsafar kasuwanci sabuwa ce.

Wang Cheng ya ce, baya ga bude wani yanki da ake cudanya da juna a farfajiyar, mataki na gaba shi ne, sayen wasu kananan motocin sayar da askirim don sayarwa a wasu sassan garin Yining. Bugu da kari, yana kuma shirin zabar wurare uku a duk fadin kasar, don kafa wuraren adana askirim kai tsaye. A cewarsa, "ya kamata wannan furannin na kankara su yi fure a ko ina a cikin kasar nan."

A lokacin kaka, jihar Xinjiang ta shiga cikin yanayin yawon bude ido mafi girma, Ma Yinyin, mai hidimtawa masu yawon shakatawa a gidajen manoma, ita ma ta soma fama da aiki. Gidan Ma Yinyin yana sabon kauyen Guniden dake garin Utubragg na birnin Bole na yankin Bortala mai cin gashin kai na Mongoliya, wanda ke da nisan kilomita 3 kadai daga tashar jirgin kasa, yanayin wurin na da kyau kwarai.

A shekarar 2016, aka kaurar da kauyen Guniden zuwa sabon wuri. Bayan shekara guda, kwatsam, sai wani kyakkyawan kauye ya bayyana, kuma canje-canje da yawa sun faru a rayuwar mazauna kauyen.

Ma Yinyin ta halarci ayyukan bincike a waje da kauyen ya shirya, inda ta koyi fasahohin gudanar da yawon shakatawa a gidajen manoma, kuma nan da nan ta fara aiwatar da aikin.

Bisa kwarin gwiwa daga Ma Yinyin da kuma jami’an kauyen, an kara bude sabbin masaukan baki a gidajen manoma. A yanzu haka, tsarin sana’o’in dake dora muhimmanci kan yawon bude ido a kauyen, na samun bunkasuwa sannu a hankali a wurin.

A jihar Xinjiang, labaran kasuwanci na talakawa masu yawa suna kara wa mutane kwarin gwiwa. A cikin wadannan labaran, hadin kai, kirki da imani ko da yaushe, su ne manyan mabudin dake iya bude kofa zuwa ga ingantacciyar rayuwa. (Bilkisu)