logo

HAUSA

Ranar Sayayya Ta Black Friday Ta kasance Ishera Ga Amurka A Wasu Fannoni

2020-11-30 20:39:31 CRI

Ranar Sayayya Ta Black Friday Ta kasance Ishera Ga Amurka A Wasu Fannoni

Kwanan baya, alkaluman da wata hukumar nazarin bayanai ta kasar Amurka wato RetailNext sun ruwaito cewa, yawan wadanda suka yi sayayya a shago a ranar sayayya ta Black Friday a bana ya ragu da 48% bisa makamancin lokacin na shekarar bara, sa’an nan yawan kudaden da aka samu a fannin sayar da kaya ya ragu da kashi 3 cikin kashi 10. Sakamakon raguwar yawan masu sayayya a shago da kusan 50%, ya sanya ayar tambaya cewa, me ke faruwa a Amurka?

Dalili na kai tsaye shi ne sake barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Kana wasu sun yi sayayya ta yanar gizo. Amma abun da yake addabar mutane shi ne koma baya a fannin yin sayayya. Alkaluman da ma’aikatar kwadago ta Amurka ta fitar sun nuna cewa, daga ranar 15 zuwa 21 ga wata, yawan wadanda suka gabatar da neman kudin tallafi karo na farko sakamakon rashin aikin yi, ya karu da dubu 30 bisa na ranar 8 zuwa 14 ga wata, adadin da ya kai zuwa dubu 778 baki daya. Illolin da annobar ta COVID-19 take haifawa suna yin kamari a wasu fannoni.

A cikin rabin shekara ko fiye da haka da suka wuce, mahukuntan Amurka sun mayar da siyasa a gaban rayukan al’umma. Matakai maras dacewa da suka dauka ba ta hanyar kimiyya ba wajen dakile da kandagarkin annobar, sun fara kawo illa a kasar, alal misali, gazawa wajen farfado da tattalin arziki, rufe kamfanoni masu yawa, karuwar yawan marasa aikin yi, da karuwar gibin da ke tsakanin matalauta da masu kudi. Duk da haka talakawa su ne suka fi dandana kudarsu, musamman ma wadanda suke fama da karancin kudin shiga.

Yaya za a dakile yaduwar annobar? Yaya za a hana karin Amurkawa rasa aikin yi? Yaya za a karfafa gwiwar masu sayayya da farfado da tattalin arziki? Kamata ya yi shugabannin Amurka su yi tunani sosai kan abubuwan da suka faru a ranar sayayya ta Black Friday ta bana. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan