logo

HAUSA

Rungumar kyawawan sassan muhalli cikin awoyi 2 a ko wane mako yana taimakawa lafiyar mutane a jiki da tunani

2020-11-29 19:20:25 CRI

Wani sakamakon nazari da aka gudanar cikin mutane masu yawa ya nuna cewa, daukar awoyi a kalla 2 a ko wane mako wajen rungumar kyawawan sassan muhalli, kamar zuwa wuraren shan iska a birane, filayen ciyayi, tsaunuka, bakin teku da dai sauransu, yana taimakawa wajen kiwon lafiyar mutane a jiki da ma tunani.

Masu nazari daga jami’ar Exeter ta kasar Birtaniya da jami’ar Uppsala ta kasar Sweden sun kaddamar da sakamakon nazarinsu cikin mujallar Scientific Reports ta Birtaniya a kwanakin baya, inda suka nuna cewa, sun tantance bayanan da suka shafi mutane kusan dubu 20 da ke yankin Scotland, kuma sun gano cewa, in an kwatanta su da wadanda ba su taba rungumar kyawawan sassan muhalli ba, mutanen da su kan dauki awoyi 2 a ko wane mako suna rungumar kyawawan sassan muhalli, kamar zuwa wuraren shan iska a birane, filayen ciyayi, tsaunuka, bakin teku da dai sauransu, sun fi samun koshin lafiya a jiki da ma tunani. Amma idan tsawon lokacin rungumar kyawawan sassan muhalli bai kai awoyi 2 a ko wane mako ba, to, ba zai amfana wa lafiyar mutane sosai ba.

Masu nazarinsu sun yi nuni da cewa, yayin da suka gudanar da nazarinsu, sun yi la’akari da jinsin wadannan mutane, ayyukansu, lafiyarsu da kuma kudaden da suke da su da dai sauransu.

Sanin kowa ne cewa, rungumar kyawawan sassan muhalli yana amfanawa lafiyar mutane a jiki da ma tunani. Amma da ma mutane ba su san yadda zai isshe su ba. Nazarin da masu nazari na kasashen Birtaniya da Sweden suka gudanar ya nuna cewa, yawancin mutane su kan je wuraren da ke da nisan kilomita 3.2 daga gidajensu don rungumar kyawawan sassan muhalli. Don haka yawo a filin ciyayi a birane, zai amfana wa lafiyar mutane a jiki da ma tunani. Hakika dai, mutane suna iya zuwa wuraren shan iska a birane, filayen ciyayi, tsaunuka, bakin teku da dai sauransu sau da dama a ko wane mako, yayin da suke iya daukar awoyi 2 sau daya a ko wane mako suna rungumar kyawawan sassan muhalli. Daukar awoyi 2 a ko wane mako wajen rungumar kyawawan sassan muhalli, ba wani abu mai wuyar aikatawa ba ne.

Dangane da sakamakon nazarin, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana bayani da cewa, wannan nazari ya bai wa likitocin shaida. Likitoci za su ba da shawarar rungumar kyawawan sassan muhalli a ko wane mako, kamar yadda suka shawarci a motsa jiki a ko wane mako. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan