logo

HAUSA

Gundumar Pingtang ta kama hanyar kawar da talauci cikin sauri

2020-11-27 13:45:03 CRI

Gundumar Pingtang ta kama hanyar kawar da talauci cikin sauri

Galibin mutane ba su san gundumar Pingtang dake lardin Guizhou, amma na’urar hangen sararin sama mai aiki da wutar lantarki ta FAST, wato irin wannan na’ura mafi girma a duk duniya tana cikin gundumar. A lokacin da ake yin gwagwarmayar yaki da talauci, mutanen gundumar su ma sun yi hangen nesa, sun kama hanyar kawar da talauci, da kuma samun arziki cikin sauri.

Ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana don gane da wannan batu.

A kauyen Changhe na karamin garin Kapu, na kabilar Maonan dake gundumar, Shi Peixiang da matarsa Meng Renlan sun noma yaji a gonaki masu fadin hekta 0.33, sun girbe yajin bayan da suka yi kokarin kulawa da shi cikin tsawon watanni biyu. Shi Peixiang ya ce, ya noma yaji bisa kwangila, sabo da haka, bai damu da matsalar sayar da yajin ba. Shi Peixiang ya kulla wannan kwangila ne da jami’ar horar da malaman kananan kabilu ta Qiannan, wadda ke da malamai da dalibai fiye da dubu 14.

Gundumar Pingtang ta kama hanyar kawar da talauci cikin sauri

A shekarar 2017, karamin garin Kapu da jami’ar sun kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa. Manoman karamin garin Kapu sun noma shuke-shuke bisa yarjejeniyar, ta yadda za a iya tabbatar da sayar da dukkan amfanin gona da manoma suka noma.

Bugu da kari, idan babu aiki da yawa a gonaki, Shi Peixiang da matarsa su kan yi aiki a wani kamfanin sarrafa amfanin gona domin samun karin kudin shiga. Kawo yanzu, manoma da yawa suna aiki a kamfanoni 4 da aka kafa a garin Kapu. Sannan gwamnatin karamin garin Kapu ta kulla yarjejeniyoyin noma yaji da wadannan kamfanoni, sakamakon haka, yawan karin kudin da manoman garin za su iya samu a duk shekara zai kai kudin Sin Yuan miliyan 5 zuwa miliyan 6.

Idan ka kai ziyara wani kauye daban na Xindian, wanda ke karamin gari na Tangbian a gundumar Pingtang, za ka ga wani babban filin ciyayi da ba a san iyakarsa ba. Manoman wurin suna girbin ciyayi, domin samar wa wani kamfanin kiwon shunu abinci. Shanu sun fi son cin irin wannan ciyayi na King Bamboo. Yanayi da tabo na wurin, suna dacewa da noman irin wannan ciyayi ta King Bamboo.

A ganin Liang Anzhi, wani manomin kauyen Xindian, wannan ciyayi na King Bamboo suna da daraja sosai. Ya dauki ciyayin yana farin ciki, yana mai cewa, “zan iya samun kudi wajen yuan 18 daga wannan kunshi daya na ciyayin King Bamboo. Ba ciyayi ba ne, zallan kudi ne.”

A da, dukkan mazauna kauyen Xindian sun sani, “Kauyen Xindian yana nesa da gari, ba a iya samun kudi daga gonakin kauyen.” Yanzu kowane magidanci yana noman irin wannan ciyayi na King Bamboo a dukkan filayen dake kewayensa, ciyayin sun kuma kawo wa manoman kauyen arziki.

Manoman kauyen su kan isar da ciyayin King Bamboo wani babban kamfanin kiwon shanu dake kusa da kauyen, inda ake kiwon shanu irin na Simmental da na Angus. Wannan kamfanin kiwon shanu yana hadin gwiwa da kauyuka, wadanda suke kusa da shi, wato kamfanin ya yi amfani da ciyayin da manoman kauyukan suke samar masa, tare da daukar ma’aikata daga kauyuka, ta yadda manoman kauyukan, musamman wadanda suke fama da kangin talauci za su samu aikin yi, har ma su samu arziki.

Gundumar Pingtang ta kama hanyar kawar da talauci cikin sauri

Yanzu haka, ana kiwon shanu fiye da dari 6 a kamfanin, sannan yawan ma’aikatan dake aiki a kamfanin ya kai 26, kuma 22 daga cikinsu su masu fama da kangin talauci ne a da. Alal misali, Ao Yuanlin daya ne daga cikinsu. Ba ma kawai Ao Yuanlin yana aiki a kamfanin ba ne, har ma shi kansa ya yi hadin gwiwa da kamfanin, wato ya ari shanu mata masu ciki guda 9 yana kiwon su a gida.

Bisa yarjejeniyar da ya kulla da kamfanin, yana daukar abincin shanu daga kamfanin, bayan jariran shanun sun girma, zai mayar da su kamfanin, sai kamfanin ya biya shi kudin Sin yuan dubu 8. Sakamakon haka, Ao Yuanxiang ba ya fuskantar hadari ko kadan. Kawo yanzu,  wannan kamfanin kiwon shanu ya riga ya samar wa manoma shanu masu ciki fiye da 120, sabo da haka, manoman wurin za su iya samun karin kudin shiga da yawa.

Kamar yadda a kan ce, idan sana’o’i sun samu ci gaba, tattalin arziki zai karu. Idan an samu riba daga sana’o’i, ana iya samun arziki. A gundumar Pingtang, an yi gwagwarmayar yaki da kangin talauci ta hanyar bunkasa sana’o’i daban daban, sakamakon haka, a watan Maris na bana, gundumar, da ma kauyuka 69 dake karkashinta, sun samu nasarar janye sunayensu, daga gundumomi, da kauyuka masu fama da kangin talauci.

A waje daya, mutane 97,779 daga magidanta 22,965 na gundumar, sun samu cin nasarar kawar da kangin talauci. Yanzu haka, yawan kudin shiga da kowane manomin gundumar zai iya samu ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu 11, maimakon wajen yuan dubu 6.67 a duk shekara. (Sanusi Chen)