logo

HAUSA

Ko hulda tsakanin kasashen Turai da Amurka za ta gudana yadda ya kamata bayan ta yi musu satar bayanai?

2020-11-26 19:02:30 CRI

Ko hulda tsakanin kasashen Turai da Amurka za ta gudana yadda ya kamata bayan ta yi musu satar bayanai?

A kwanakin baya hukumar kula da harkokin kasar Amurka ta sanar da cewa, shugaban kasar Amurka mai jiran gado ‘dan jam’iyyar Democrat Joseph Biden ya lashe babban zaben shugabancin kasar da aka shirya, daga baya Biden ya buga waya ga shugabannin kungiyar tarayyar Turai da na kungiyar NATO, inda ya jaddada cewa, zai kara kafafa huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Turai, har ma wasu kafofin watsa labarai sun bayar da rahotanni cewa, sassan biyu wato Amurka da kasashen Turai za su kyautata huldar dake tsakaninsu, shin ko hakan zai faru?

Kafofin watsa labaran kasar Denmark sun fayyace cewa, kasar Denmark a baya ta yi shirin sayen wasu sabbin jiragen saman yaki tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, amma ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta sa ido kan ma’aikatar baitulmalin kasar da ma’aikatar harkokin wajen kasar da sauran hukumomin gwamnatin kasar, da ma wasu kamfanonin samar da makamai na kasar, ta hanyar yin amfnai da huldar hadin gwiwar dake tsakaninta da Denmark a bangaren samar da bayanan sirri, ban da haka, hukumar leken asirin Amurka ita ma ta saci bayanan sirri na kamfanonin samar da makamai guda biyu na kasashen Turai, wadanda suka yi takarar sayar da jiragen saman yaki ga Denmark, a karshe, kamfanin Lockheed Martin na Amurka ya yi nasarar sayar da jiragen saman yakinsa samfurin F-35 ga Denmark. Baya ga kasar Denmark, Amurka tana sa ido kan hukumomin kasashen Sweden da Jamus da Faransa da Norway da Netherlands da sauran kasashen Turai.

A don haka, zai yi wahala sassan biyu wato Amurka da kasashen Turai su gudanar da hulda tsakaninsu kamar yadda suka yi a baya, abu mai muhimmanci shi ne, yanzu haka kasashen Turai suna kara nuna bacin rai ga Amurka, kuma suna taka tsan-tsan wajen gudanar da huldar dake tsakaninsu da Amurka. Wannan ya sa watakila huldar dake tsakanin sassan biyu za ta kyautata, amma saboda sabanin dake tsakaninsu wadanda da kyar a warware su, ana iya cewa, akwai babbar matsala kafin a sake farfado da wannan hulda a nan gaba.(Jamila)