logo

HAUSA

Ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin kiwon lafiya

2020-11-26 19:55:32 CRI

Ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalolin kiwon lafiya

Annobar COVID-19 ta sauye al’amura da dama, ciki har da yadda bil Adama ke gudanar da harkokin sa na yau da kullum, musamman ma fannin cudanyar jama’a, da manufofin kiwon lafiyar kasashe.

Yayin da ake shirin kara rungumar matakan rayuwa tare da COVID-19, abubuwan tambaya sun hada da wadanne irin darussa ne wannan annobar ta zo wa duniya da su? Wane muhimmanci ya dace duniya ta dora kan shawo kan annobar ta fuskar kandagarki da binciko magunguna?

A bana, bullar cutar COVID-19, ya gwada karfin tsarin kiwon lafiyar kasashe da dama, ba tare da la’akari da karfin ci gaba ko akasanin hakan ba. Masharhanta da dama na ganin sashen kiwon lafiya a mataki na farko, a matsayin fannin da ke taka rawar gani a bangaren yaki da wannan annoba.

Kaza lika a hannu guda, annobar COVID-19 ta bijirowa gwamnatocin kasashen duniya da damammaki na sake nazari, tare da sauya akalar tsarin su na kiwon lafiyar al’umma, ta hanyar gano sassa mafi muhimmanci sama da saura. Don haka dai ana iya cewa, tushen tsarin kiwon lafiya na daukacin bil adama, na komawa ne ga ingancin tsarin kiwon lafiya a matakin farko.

A bangaren kasashen da suka ciri tuta wajen amfani da dabarun zamani don shawo kan annobar akwai kasar Sin, wadda ta rungumi hikimomin kimiyya da fasaha, da kyautata manufofin kiwon lafiya, don magance kalubalolin da ta gamu da su, lokacin da take tsaka da yaki da wannan annoba.

Bugu da kari, karkashin manufofin ta na yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, a fannin bunkasa kayayyakin more rayuwa, da kyautata tsarin kiwon lafiya, da raba fasahohi, da dabaru, kasashen Afirka sun ci gajiya mai tarin yawa.

Masu fashin baki na hasashen cewa, a yayin taron dandalin ministocin kiwon lafiya na Sin da Afirka dake tafe a badi, za a kara maida hankali sosai game da kara bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, wajen kara kyautata tsarin kiwon lafiyar jama’a tun daga matakin farko.

Kaza lika, akwai yiwuwar karfafa hadin gwiwar sassan biyu ta fuskar samar da sabon ci gaba a bangaren ayyuka da tsare tsare, da kyautata musaya tsakanin masana, da inganta kwarewa, da samar da kudade na gina sanin makamar aikin ma’aikatan lafiya.

A matsayin su na sassa masu tasowa, Sin da nahiyar Afirka, za su cimma nasarorin da suka sanya gaba, na kyautata kiwon lafiyar al’ummun su, muddin sun yi hadin kai yadda ya kamata. Kaza lika duniya baki daya, za ta ci gaba da samun nasara kan annobar COVID-19, muddin dai matakan da aka fara aiwatarwa na hadin gwiwar samar da rigakafi, da na kandagarkin bazuwar cutar suka dore.

Burin duniya a wannan yanayi dai bai wuce fatan “Gudu tare a tsira tare ba!