logo

HAUSA

Bude kofa ga juna shi ne muhimmin matakin raya ayyukan APEC

2020-11-25 09:55:08 CRI

A farkon makon da ya gabata aka bude taron mambobin kungiyar hadin gwiwa ta yankin Asiya da Fasifik (APEC) na shekarar 2020, inda yayin taron ministocin kasashen na APEC da ya gudana ta kafar bidiyo, suka jaddada kudurinsu na gudanar da ciniki da zuba jari cikin ’yanci, tare da kara himmantuwa wajen farfado da tattalin arzikin yankin daga mummunan tasirin annobar COVID-19.

Bude kofa ga juna shi ne muhimmin matakin raya ayyukan APEC

Ministan kula da cinikayya da kasashen waje na kasar Malaysia, Mohamed Azmin Ali, wanda ya jagoranci taron ministocin ya nanata bukatar kasashe mambobin kungiyar, su ci gaba da adawa da kariyar cinikayya, tare da karfafa tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Taron ministocin ya gudana ne gabanin taron shugabannin kasashen kungiyar, wanda shi ma aka aiwatar ta kafar bidiyo, wanda kuma ya share fagen amincewa a hukumance, da burin da kungiyar ke da shi bayan shekarar 2020.

Da yake tsokaci game da matsayar kasar Sin, a yayin taron shawarwari na shugabannin masana’antu da cinikayya na kungiyar ta APEC ta kafar bidiyo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a wannan shekarar, kasar Sin ta gabatar da karin wasu manufofi na bude kofarta ga kasashe daban daban, wannan wata manufa ce da ta dace da moriyar mambobin kungiyar ta APEC da ma sauran kasashen duniya baki daya.

Bude kofa ga juna shi ne muhimmin matakin raya ayyukan APEC

Xi ya kara da cewa, akwai bukatar da kasashe su taimakawa juna yayin da suke cikin mawuyacin hali, su rungumi akidar hadin gwiwa, da karfafa munafar tuntubar juna, da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19, da gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da kokarin ganin bayan annobar COVID-19 cikin gaggawa, da samun dawaumamman ci gaba mai dorewa, da ci gaban tattalin arzikin duniya da zai kunshi kowa da kowa.

A shekarar 1989 ne dai aka kafa kungiyar APEC da nufin bunkasa cinikayya da raya tattalin arziki, da zamantakewar mambobinta. Kuma kawo yanzu tana da mambobi 21.

Bude kofa ga juna shi ne muhimmin matakin raya ayyukan APEC

Ya zuwa yanzu mambobin APEC na da kaso 50 bisa dari na jimillar GDPn kasashen duniya baki daya, da yawan mutane da ya kai biliyan uku. Kaza lika GDPn su ya karu daga dala tiriliyan 19 a shekarar 1989, zuwa dala tiriliyan 42 a shekarar 2015.

Alal hakika, kowa na iya fahimtar cewa, amincewar da mambobin APEC suka yi, su budewa juna kofa, da inganta hadin gwiwar su ne ya haifar da dukkanin wadannan nasarori da kungiyar ta cimma kawo wannan lokaci. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)