logo

HAUSA

Duniya Za Ta Amfana Da Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Kasar Sin

2020-11-25 19:16:37 CRI

Duniya Za Ta Amfana Da Ayyukan Binciken Duniyar Wata Na Kasar Sin

A ranar Talata 24 ga watan Nuwanban shekarar 2020 ne, kasar Sin ta yi nasarar harba na’urar bincike ta Chang'e-5, a wani aiki da ya kasance mafi sarkakiya cikin jerin ayyukan binciken duniyar wata da kasar ta aiwatar, binciken da ya kara bude wani sabon babi a harkar binciken sararin samniya.

Duk da cewa, ita ce kasa ta uku, bayan Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet da suka gudanar da bincike a duniyar wata, kasar Sin ta sha alwashin raba samfuran da na’urar za ta dawo da su doron duniyarmu tare da sauran sassa gami da masu binciken sararin samaniya

Idan har wannan aiki ya yi nasara, zai kasance irinsa na farko da ya kunshi dauko samfura daga duniyar wata, tun bayan da Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet suka gudanar a shekarun 1960 da 1970.

Duba da muhimmancin hakan ta fuskar binciken kimiyya. Masana na cewa, binciken sararin samaniya aiki ne da ke shafar rayuwar daukacin bil Adama, duk da haka kasar Sin na fatan bunkasa shi ta hanyar musaya, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Abin da ke kara bayyana kiraye-kirayen kasar Sin na yin hadin gwiwa da samun nasara tare.

Bugu da kari, wannan mataki na kasar Sin, ya kara nuna muhimmancin cudanyar bangarori da kasar ke fatan ganin ya kankama. Hannu daya, in ji masu iya magana, ba ya daukar Jinka.

Kasar Sin ta sake bayyana kudirinta na yin aiki tare da sauran kasashe, don ba da gagarumar gudummawa kan yadda za a gudanar da ayyukan bincike da yadda zai amfani bil-Adama cikin lumana, da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama

Shin ko sauran kasashe, za su yi koyi da kasar Sin wajen gudanar da ayyukan bincike da cin gajiyar sararin samaniya cikin lumana ga daukacin bil-Adama? Rana aka ce ba ta karya, sai dai Uwar Diya ta ji Kunya. Kasar Sin dai ba za ta sauya manufarta ta samun ci gaba cikin lumana, ba. (Ibrahim Yaya)