logo

HAUSA

Sin da Afirka na hada kansu domin yaki da cutar COVID-19

2020-11-25 11:30:15 CRI

Sin da Afirka na hada kansu domin yaki da cutar COVID-19

Cutar numfashi ta COVID-19 ta barke tsakanin kasa da kasa a bana, wadda ta haifar da matsaloli da dama ga kasashen Afirka. Shi ya sa, bisa gayyatar da wasu kasashen Afirka suka yi mata, kasar Sin ta tura tawagogin likitoci ga wasu kasashen nahiyar, domin samar musu taimako wajen yaki da cutar. A sa’i daya kuma, tawagar likitoci rukuni na 21 da lardin Hunan na kasar Sin ya tura wa kasar Saliyo, ta ci gaba da gudanar da ayyukan ba da jinya a kasar, bayan ta kammala wa’adin aikinta, domin ba da taimakon yaki da cutar COVID-19.

Ga karin bayani da wakilinmu Saminu Alhassan ya hada mana:

Bisa shirin da aka tsara, tawagar likitoci rukuni na 21, za ta koma kasar Sin ne bayan ta kammala wa’adin aikinta a bana, amma, barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ba zato ba tsammani, ta sa likitocin tawagar sun tsai da kudurin ci gaba da gudanar da aikin jinya a kasar Saliyo, domin taimakawa kasar wajen yaki da wannan annoba.

Tawagar tana aiki a asibitin zumunci na Sin da Saliyo da kasar Sin ta ba da taimako wajen ginawa, wanda ya zama asibiti mafi inganci a kasar. Bayan barkewar cutar, an mayar da wannan asibiti, a matsayin asibitin musamman dake karbar masu fama da cutar numfashi ta COVID-19. Amma, a farkon barkewar cutar a kasar Saliyo, karancin kayayyakin jinya ya taba zama babbar matsala dake gaban likitocin tawagar, daga bisani, kayayyakin yaki da cutar da kasar Sin ta aika zuwa kasar Saliyo, sun ba su babban taimako wajen warware wannan matsala.

Shugaban tawagar likitoci, Jiang Haibo ya ce, sabo da isar wadannan kayayyakin kandagarki da aka tura musu, sun kai ga gudanar da aikin jinya tare da kiyaye lafiyar kansu. Sa’an nan, tawagar ta kasance tawagar likitoci daya tilo a kasar Saliyo dake iya ba da jinya ga masu kamu da cutar kai tsaye, jami’an ta kuma na iya shiga dakunan da aka kebe musamman domin masu fama da cutar numfashi ta COVID-19.

A sa’i daya kuma, likitocin tawagar su kan yi mu’amala da takwarorinsu na kasar Sin, domin kara fahimtar su game da sabbin bayanan yaki da cutar, sa’an nan, su sanar da bayanan ga kasar Saliyo, domin dakile ci gaba da yaduwar cutar.

Bisa kokarin da suka yi, gaba daya, an karbi masu fama da cutar COVID-19 mai tsanani guda 77, a asibitin zumunta na Sin da Saliyo, kuma mutane 72 sun warke daga cutar. A sa’i daya kuma, babu wani likita na Sin ko Saliyo dake aiki a wannan asibiti, wanda ya kamu da cutar COVID-19, lamarin da ya zama abin alfahari kwarai da gaske a kasar Saliyo.

Tun daga shekarar 1973, lokacin da kasar Sin ta fara tura tawagar likitoci zuwa kasar Saliyo, ya zuwa yanzu, shekaru sama da 40 ke nan da suka gabata, tawagogin Sin sun samu yabowa matuka daga wajen al’ummomin kasar. Har ma shugaban tawagar likitoci rukuni na 21 Jiang Haibo ya bayyana cewa, dukkanin al’ummomin kasar Saliyo, suna fari ciki sosai a lokacin da suka hadu da likitocinmu, su kan gaishe mu, ko kuma su dauki hotuna tare da mu.

A halin yanzu, hadin gwiwar kasar Sin da kasar Saliyo a fannin kiwon lafiya ta zama muhimmin mataki, wanda ke tallafawa al’ummomin kasar Saliyo kwarai da gaske. (Maryam)