logo

HAUSA

An yaba da rawar da Sin ke takawa kan hadin gwiwar kasa da kasa

2020-11-25 18:51:52 CRI

An yaba da rawar da Sin ke takawa kan hadin gwiwar kasa da kasa

A kwanakin baya an kammala taron kasa da kasa game da “fahimtar kasar Sin” mai taken “manyan sauye-sauye da babbar jarrabawa da hadin gwiwa: sabon burin zamanantar kasar Sin da kyakkyawar makomar bil Adama” na shekarar 2020 a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda ta kafar bidiyo tsohon firayin ministan kasar Birtaniya James Gordon Brown ya yaba da rawar da kasar Sin take takawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, yana mai cewa, ganin yadda yanzu haka ake fama da matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da koma bayan tattalin arziki, bai dace wasu kasashe su yi kokarin kare muradun kansu kawai ba.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, wasu ‘yan siyasar kasar Amurka suna aiwatar da manufar bangaranci, kana sun yi zalunci wasu kasashe yayin gudanar da harkokin cinikayya, tare da zargin sakamakon wayewar kan wasu kasashe, matakin da ya haifar da hadari yayin raya tattalin arzikin duniya da kuma gudanar da harkokin kasa da kasa.

Har kullum manyan sauye-sauye su kan haifar da babbar jarrabawa, duk da cewa, ana fuskantar rikice-rikice da dama, amma bai dace a canja muradun zamaninmu na shimfida zaman lafiya da samun ci gaba ba, kuma ba zai yiyu a hana yunkurin habakar tattalin arziki a fadin duniya ba, gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da gudanar da cinikayya maras shinge sun dace da moriyar kasa da kasa, manyan ‘yan siyasar kasashen duniya su ma sun yaba da kokarin da kasar Sin take yi a wannan bangare.

Kana abun da ya fi jawo hankalinsu shi ne, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka domin kandagarkin annobar COVID-19 da warware kalubalolin dake gabanta, wato ta sa kaimi kan kwaskwarima a cikin kasar ta hanyar bude kofa ga ketare, kuma ta ingiza ci gaban kasar ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 27 ta kafar bidiyo cewa, kasar Sin za ta duba yiwuwar shiga yarjejeniyar CPTPP, lamarin da ya alamta cewa, kasar Sin ta amince da daukacin yarjejeniyoyin cinikayya maras shinge wadanda za su ingiza habakar tattalin arzikin shiyya shiyya da kuma fadin duniya.

Hakika nacewa kan bude kofa da hadin gwiwa, yana da muhimmanci matuka yayin da ake fuskantar kalubaloli, ko shakka babu matakan da kasar Sin ta dauka za su ba da jagora ga kasashen duniya yayin da suke kokarin tabbatar da wadata da ci gaba.(Jamila)