logo

HAUSA

Amurka na fakewa da guzuma ta harbi karsana

2020-11-24 17:24:24 CRI

Amurka na fakewa da guzuma ta harbi karsana

Kasar Sin ta bukaci Amurka ta gaggauta dakatar da dabi’arta ta fakewa da kare tsaron kasa wajen matsawa kamfanonin kasashen waje. Wannan na zuwa ne bayan samun wasu rahotanni dake bayyana niyyar Amurkar ta hana sayar da wasu kayayyakin fasaha ga kamfanonin kasar Sin 89.

Har kullum, Amurka kan yi zargi ko yada jita-jita ba tare da gabatar da shaidu ba, inda take fakewa da “tsaron kasa” wajen kakaba takunkumi ko matsawa kamfanonin kasashen waje. A matsayinta na babbar kasa, bai kamata ta rika zubar da kima da darajarta tana nuna yatsa ba tare da kwararan dalilai ko hujjoji ba. Abun da har yanzu gwamnatin Trump ta kasa fahimta shi ne, yadda wadannan matakai ko mummunar dabi’a za su zubar da kima tare da darajar kasar a idon al’ummar duniya.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin a matsayinta na mai tasowa, ta jajirce inda take ta samun saurin ci gaba ta kowacce fuska, lamarin da Amurka ke gani a matsayin barazana ga kasancewarta kasa mafi karfi a duniya. Sai dai, abubuwa sun sauya a yanzu, kai ya waye kuma idanun al’ummun duniya sun bude, an shiga wani yanayi da kowacce kasa ke kokarin dogaro da kanta wajen samun ci gaba. Kuma a wannan lokaci, ya zama wajibi dukkan kasashe su fahimci cewa, adalci a tsakaninsu, shi ne hanya mafi dacewa, bai wai kokarin tauyewa ko dankwafe wata kasa daga samun ci gaba ba.

Ko a makon da ya gabata, gwamnatin Trump ta bayar da wani umarnin hana zuba jari a wasu kamfanonin kasar Sin, tana ikirarin kamfanonin mallakar rundunar sojin kasar Sin ne. Amurka ta bayyana haka ne tare da daukar matakin, ba tare da gabatar da wata shaida ba. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, wadannan matakai na Amurka, sun sabawa ka’idar takara a kasuwa da dokokin cinikayya na kasa da kasa, haka kuma za su zubar da kimar Amurka a duniya. Ya ce Sin na kiyaye dokoki da ka’idoji yayin da take gudanar da kasuwanci, haka kuma tana kiyaye dokoki da ka’idojin kasashe daban-daban, ciki har da Amurkar.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, za ta nemi ci gaba bisa gaskiya da adalci da kiyaye dokoki, haka kuma ba za ta taba neman karin karfi ko zama barazana ga wata kasa ba. A don haka, idan har Amurka na daukar Sin a matsayin barazana, to kamata ya yi ita ma ta dukufa wajen neman raya kanta ba wai dankwafe wasu ba, ko fakewa da tsaron kasa wajen matsawa kamfanoni.

A matsayin manyan kasashe, hadin gwiwa da daukar darasi daga juna su ne za su haifar musu da alfanu dama duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)