logo

HAUSA

Masanan Afirka: Nasarar Kawar Da Kangin Talauci Da Kasar Sin Ta Samu Za Ta Amfani Afirka

2020-11-24 14:19:12 CRI

Game da labarin da aka bayar cewa, an fitar da dukkan gundumomi 832 na kasar Sin daga halin fama da kangin talauci, masana da kwararru na kasashen Afirka, sun nuna yabo sosai, har ma sun ce, nasarar kawar da kangin talauci da kasar Sin ta samu za ta amfani kasashen Afirka sosai.

Masanan Afirka: Nasarar Kawar Da Kangin Talauci Da Kasar Sin Ta Samu Za Ta Amfani Afirka

Adhere Cavince wanda yanzu yake karatu yake neman digiri-digiri a jami’ar horar da malamai ta Huazhong ta kasar Sin, bai iya komawa jami’a ba tukuna sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a bana. Adhere Cavince ya taba kawowa birnin Beijing da jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ziyara karo na farko a shekarar 2018 a matsayin wani mamban tawagar wakilan maneman labaru ta kasarsu. Adhere Cavince ya ce, “Babban ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman nasarar da ta samu a fannin kawar da kangin talauci a yankunan kauyuka ya burge ni sosai. Sannan abin da ya fi burge ni shi ne, manoma sun yi kasuwanci sun samu kudin shiga bisa taimakon hukumomin gwamnati.”

Adhere Cavince yana ganin cewa, sauran kasashen duniya za su ci gajiyar nasarar da kasar Sin ta samu wajen kawar da kangin talauci.

“A lokacin da ake aiwatar da babban shirin bunkasa kasar Sin a cikin shekaru 5 da suka gabata, daukacin al’ummar Sinawa sun samu nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar. Ba ma kawai wannan wani albishi ne ga kasar Sin ba, har ma yana da matukar muhimmanci ga duk duniya. Ya alamta cewa, an samu ci gaba wajen aiwatar da burin neman dawaumammen ci gaba da MDD ta tsara. A ganina, kasar Sin ta samu nasarar taimakawa dimbin mutane fita daga kangin talauci cikin gajeren lokaci, ba abu mai sauki ba. Idan da a ce kasar Sin ba ta samu irin wannan nasara ba tukuna, ke nan, ana bukatar albarkatun duk duniya domin taimakawa Sinawa wajen su yi yaki da kangin talauci.”

Dorine Nininahazwe, wata ’yar kasar Burundi ce wadda ke kula da sashen kungiyar “One Campaign” dake gabashin Afirka. Ta yi shekaru 10 tana aikin kawar da talauci. Ta taba shan binciken yadda ake kokarin kawar da kangin talauci a wasu yankunan yammacin kasar Sin. Dorine Nininahazwe ta bayyana cewa, kasar Sin ta dauki dimbin matakan kawar da talauci masu amfani kuma masu alaka da aikin gona, da kiwon lafiya da koyarwa da dai makamatansu, wannan ya kasance kamar abin koyi ne ga kasashen Afirka.

Masanan Afirka: Nasarar Kawar Da Kangin Talauci Da Kasar Sin Ta Samu Za Ta Amfani Afirka

"Idan an duba nauyin farko dake cikin babban shirin kawar da kangin talauci da kasar Sin ta tsara, za a iya gane cewa, kasashen Afirka ma za su iya yin haka. Tsara wani shiri, da kuma tabbatar da nauyin farko da ke bisa wuyanmu, shi ne aikin da ake yi a ko ina. Sannan mu ma za mu iya kafa wani tsarin adana bayanai mai alaka da aikin kawar da kangin talauci. Bugu da kari, mu ma ya kamata mu tsara wani tsarin sa ido kan yadda ake yaki da kangin talauci. Talauci dai iri daya a duk duniya. Sabo da haka, za mu iya koyon fasahohi da yawa daga takwarorinmu Sinawa.”

Peter Kagewanja, shugaban cibiyar nazarin manufofin Afirka ta kasar Kenya ya bayyana cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata bayan kaddamar da manufofin yin kwaskwarima a gida da bude kofarta ga ketare, ba ma kawai kasar Sin ta ci nasarar kawar da kangin talauci ba, har ma ta zama daya daga cikin kasashe masu tasowa da tattalin arzikinsu ya samu karuwa mafi sauri, wannan babbar gudummawa ce ga daukacin bil Adama.

“A cikin shekaru 40 ke nan, kasar Sin ta fitar da mutane kusan miliyan 800, wato mutane mafi yawa a tarihin daukacin bil Adama daga kangin talauci, ta bayar da gudummawarta sosai ga kokarin kawar da kangin talauci a doron duniyarmu. Na karanta wasu littattafan da shugaba Xi Jinping ya rubuta kan batun yin gwagwarmayar kawar da talauci ta hanyoyin kaddamar da manufofin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare, da karfafa gwiwar al’mmun Sinawa da su yi kokarin samun ci gaba kamar yadda al’ummun sauran kasashen duniya suke yi. Sabo da haka, Ina fatan abokai Sinawa da abokanmu na Afirka su kara yin kokari tare, ta yadda galibin Afirkawa za su iya fitar da kansu daga kangin talauci su samu arziki. Wannan zai amfana wa Afirka da kasar Sin gaba daya.” (Sanusi Chen)