logo

HAUSA

Samun Bunkasuwa Shi Ne Mabudin Warware Matsalar Talauci

2020-11-24 20:18:14 CRI

Samun Bunkasuwa Shi Ne Mabudin Warware Matsalar Talauci

A sakamakon tinkarar cutar COVID-19, tattalin arzikin duniya ya ragu. Bisa hasashen da bankin duniya ya yi, yawan mutanen da za su yi fama da talauci a duniya a shekarar 2020 zai karu, idan aka kwatanta da shekaru 20 da suka gabata, inda mutane miliyan 150 a duniya za su fada cikin talauci a sakamakon cutar COVID-19.

Yaya za a daidaita matsalar yaki da cutar da kiyaye bunkasuwar tattalin arziki da kuma tabbatar da zaman rayuwar jama’a? Yaya za a sa kaimi ga cimma burin yaki da talauci na duniya? Su ne batutuwan da kasa da kasa ke tinkara a halin yanzu.

A wannan halin da ake ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci zaman na biyu na taron koli na kungiyar G20 karo na 15 ta kafar bidiyo a daren ranar 22 ga wata, inda ya ba da ra’ayin samun bunkasuwa mai dorewa, tare da jaddada cewa, samun bunkasuwa shi ne mabudin warware matsalar talauci.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a mai da ajandar samun bunkasuwa a matsayin muhimmin aiki bisa manyen tsare-tsare na duniya, kana ya gabatar da ra’ayoyi uku wato maida aikin samun bunkasuwa a gaban kome, da daukar matakan da suka dace a dukkan fannoni, da kuma samar da yanayin tattalin arzikin duniya mai inganci, wadanda suka shaida fasahohi da ra’ayoyin Sin bayan da aka yi nazari da tunani, kuma sun bayyana abin dake kawo moriya da kuma matsala, ta yadda za a samar da shawarwari don warware matsalar bunkasuwa ta duniya.

Duk da wahalhalu da kalubalolin da ake fuskanta, gami da kokarin neman samun hanyar bunkasuwa, idar har sauran kasashe masu tasowa, suka martaba ajandar da MDD ta tsara kan neman samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, sa’an nan suka tsai da niyyar samun ci gaba, tare da mai da hankali a kan amfanawa jama’a, to su ma za su samu nasarar yaki da talauci.

Ban da samun akidar da ta dace, akwai kuma bukatar daukar matakan a zo a gani, kasar Sin ta gabatar da jerin shawarwari ga sha’anin kawar da talauci na duniya, ciki har da mara wa kasashe masu tasowa baya a fannin hada-hadar kudi, sa kaimi ga raya muhimman kayayyakin more rayuwa da aikin sadarwa, rage kariyar ciniki, da bunkasa tattalin arziki ta yanar gizo don yaki da talauci da dai sauransu.

Samun bunkasuwa gaba daya shi ne babban buri na karshe. A ranar 23 ga wata, an yi nasarar kawar da talauci a dukkan gundumomi masu fama da fatara a kasar Sin. Babu shakka, kasar Sin da ta riga ta cimma burin kau da kangin talauci shekaru 10 kafin wa’adin aikin, wadda kuma za ta shiga wani sabon matakin bunkasuwa ba da jimawa ba, za ta kara yada fifikonta wajen taimakawa kasashe masu tasowa wajen kyautata kwarewarsu ta yaki da talauci bisa karfin kansu, a kokarin raya kyakkyawar duniya da babu talauci a cikinta, har ma a samu ci gaba tare.(Zainab, Kande)