logo

HAUSA

Akwai bukatar hangen nesa yayin gudanar da harkokin kasa da kasa

2020-11-23 21:00:08 CRI

Akwai bukatar hangen nesa yayin gudanar da harkokin kasa da kasa

Tun daga ranar 17 zuwa 22 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rika halartar ganawa karo na 12 na shugabannin kasashen BRICS, da kwarya-kwaryar taro karo na 27 na shugabannin kasashen mambobin kungiyar APEC, da taron kolin shugabannin rukunin G20 karo na 15, a daidai wannan lokacin da ake fama da matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da manyan sauye-sauye a duniya, shugaba Xi ya sake gabatar da dabarun kasar Sin domin taimakawa wajen warware kalubalolin da duniya take fuskanta, tare kuma da ba da jagora kan ci gaban duniya bayan ganin bayan annobar.

Yanzu adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya zarta miliyan 57, ya zama wajibi a dakile annobar cikin sauri, a don haka shugaba Xi ya yi kira ga kasashen duniya yayin tarukan koli uku, da su mayar da moriyar jama’a a gaban kome, ya kuma jaddada cewa, hada kai da hadin gwiwa shi ne makami mai karfi na dakile annobar, kana ya bukace su da su nuna goyon baya ga hukumar kiwon lafiya ta duniya. Ya sake bayyana cewa, kasarsa za ta samar da allurar rigakafin COVID-19 ga al’ummar duniya, kowa ya ga kokarin da kasar Sin take yi, shugaban kasar Rasha Putin shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin ta shaida wa daukacin duniya cewa, ana iya hana yaduwar kwayar cutar, kasar Sin ta ba da misali wajen kandagarkin annobar.

Yanzu tattalin arzikin duniya ya shiga wahala, kasar Sin wadda ta sake dawowa bakin aiki kafin sauran kasashen duniya, ta gabatar da dabarun da ta yi amfani da su domin farfado da tattalin arzikin duniya, wadannan muhimman batutuwan dake shafar dabarun su ne: bude kofa ga ketare, da kirkire-kirkire, da yin hakuri da juna, da kuma raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, duk wadannan sakamako da kasar Sin ta samu, ko shakka babu za su ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya.

Hakika a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin ci gaban tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana kokarin tsara sabon tsarin raya kasarta, shugaba Xi ma ya sanar da cewa, ba zai yiyu ba kasar Sin ta koma baya, kuma ba zai yiyu ba kasar Sin ta raba kawunan sauran kasashe ko rufe kofarta ga ketare, kasar Sin wadda za ta shiga sabon matakin raya kasa tare kuma da nacewa kan manufar gudanar da hadin gwiwa domin samun moriya tare, za ta ci gaba da taka rawar gani wajen gudanar da harkokin kasa da kasa, haka kuma za ta ba da gudumowarta yayin da ake gina kyakkyawar makomar bil Adama ta hanyar tattaunawa tare da gina da kuma morewa tare.(Jamila)