logo

HAUSA

Kalaman Xi A Tarukan Kolin Kasa Da Kasa Sun Ja Hankalin Duniya

2020-11-23 15:58:06 CRI

Yayin da a makon da ya gabata aka kammala tarukan kolin kasa da kasa uku da suka hada da taron kolin shugabannin kasashen mambobin BRICS, da taron dandalin kawancen raya tattalin arzikin Asiya da Pacific (APEC), da kuma taron mambobi kasashen G20.

Wadannan taruka uku sun zo ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar manyan kalubaloli a sanadiyyar barkewar annobar COVID-19 wanda ya haifar da karayar tattalin arziki da shiga matsin rayuwa da wahalhalu dake addabar jama’ar kasashen duniya. Sai dai a lokacin da ya halarci muhimman tarukan, shugaba Xi Jinping, ya gabatar da shawarwari da matsayar kasar Sin game da yadda za a tinkari manyan kalubalolin duniya a yayin da ya halarci tarukan gamayyar kasa da kasar. Kamar yadda mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi karin haske kan muhimman tarukan kasa da kasar da aka gudanar a daidai lokacin da duniya ke fama da bala’in da annobar mafi muni a duniya ta haifar. Cikin sanarwar da mista Wang ya fitar, ya ambato shugaba Xi na bayyana shawarwari da matsayar kasar Sin kan matakan da ya dace a dauka domin tinkarar yaki da annobar COVID-19, gami da yunkurin inganta makomar tattalin arzikin duniya, da kyautata zaman rayuwar al’umma, wanda a cewar shugaban za a iya cimma wannann nasara ne kadai ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa a lokacin yaki da annobar da ma bayan kawo karshenta. Kasashen duniya da dama sun yi tsokaci game da kalaman da shugaba Xi ya gabatar a lokutan gudanar manyan tarukan uku. Wani muhimmin batu da ya ja hankalin duniya shi ne, furucin shugaban na batun mayar da rayukan jama’a da ci gabansu a gaban komai, da batun yin hadin gwiwa da nuna goyon bayan juna wajen yakar annobar COVID-19, da kuma batun nuna goyon baya kan rawar da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa wajen yaki da annobar ta COVID-19. Koda yake, wannan ba shi ne karon farko da shugaban ke gabatar da aniyar kasarsa na neman hadin gwiwa da kasa da kasa domin tinkarar kalubalolin dake gaban duniya ba. Har kullum, manufar kasar Sin shi ne kokarin tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban da nufin yin aikin tare, da cin moriya tare, ta hanyar hadin gwiwar bangarori daban daban karkashin sabuwar dangantaka da huldar kasa da kasa, kana da yin adawa da manufar fifita bukatu na kashin kai, domin samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama don a samar da wata duniya mai cike da zaman lafiya da adalci. (Ahmad Fagam)