logo

HAUSA

Ko Neman Gafara Yana Iya Ceton Rayukan Fararen Hula 39 a Afghanistan?

2020-11-22 17:46:39 CRI

Ko Neman Gafara Yana Iya Ceton Rayukan Fararen Hula 39 a Afghanistan?

Kwanan baya, babban kwamandan rundunar tsaron kasar Australiya Angus Campbell ya amince da laifuffukan da sojojin kasar suka aikata a kasar Afghanistan, ya kuma nemi gafara kan lamarin. A cewarsa, wasu sojoji dake sintiri sun dauki doka a hannunsu, sun saba ka’idoji, sun kitsa labari, sun yi karya, sun kuma kashe fursunoni. Sojojin na Australiya sun kashe fararen hula 39 kai tsaye ko kuma ba da umurnin kashe su a Afghanistan.

A wani bangare, babban jami’in sojan na Australiya ya amince cewa, kasarsa ta horas da sojojinta ta hanyar kashe fararen hula 39 a Afghanistan. Ya kuma nemi gafara kan laifuffukan da sojojin kasar suka aikata a Afghanistan. A wani bangare kuma, sojojin Australiya sun yi wa takwarorinsu na kasar Amurka hassada, a cewarsu, abubuwan da sojojin kasashen Birtaniya da Amurka suka aikata, sun fi muni. Amma matasan Australiya ne suka yi musu hassada, inda suka yi farin cikin ganin yadda sojojin Amurka suka ci zalin mazauna wurin.

‘Yan fashi wadanda suke kiran kansu masu wayin kai, ko da sun yi badda kama, suna kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam, amma a hakika ba su sauya ainihin halayyarsu ba har abada. Ko ba haka ba?

A ‘yan kwanakin baya, wasu ‘yan siyasan Australiya da kafofin yada labarun kasar masu son kai, suna yunkurin shafa wa kasar Sin bakin fenti, inda suka yi karyar kasar Sin. Sun kuma rura wutar nuna wa kasar Sin tsana da kin jini. Abubuwan da suka aikata sun illata huldar da ke tsakanin Sin da Austrliya.

Har ila yau Australiya ta saba manyan ka’idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, ta dauki matakan da ba su dace ba kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar kasar Sin, kamar batutuwan Hong Kong, Xinjiang da Taiwan. Ta sha jagoranta ko kuma sa shiga cikin harkokin da suka shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin a kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD, sa’an nan ta tsoma baki cikin batun kafa dokar tsaron kasa a Hong Kong na kasar Sin, ta kuma goyi bayan yunkurin yankin Taiwan na halartar babban taron WHO.

Yanzu sojojin Austrliya sun kashe rayukan fararen hula 39 a Afghanistan. Idan neman gafara yana iya ceton rayukansu, to, za a tabbatar da cewa, nan gaba sojojin Australiya ba za su sake aikata haka ba? Shin wannan shi ne yadda kasashen yammacin duniya suke kiyaye hakkin dan Adam? Gwano baya jin warin jikinsa. Lokaci ya yi da Australiya za ta warware matsalar da take fuskanta a fannin kare hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)