logo

HAUSA

Gina al’umma mai makoma ta bai daya a yankin Asiya da tekun Fasifik zai bude sabon babi ga hadin-gwiwar kasashen yankin

2020-11-21 20:55:57 CRI

Gina al’umma mai makoma ta bai daya a yankin Asiya da tekun Fasifik zai bude sabon babi ga hadin-gwiwar kasashen yankin

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sake bada shawarar gina al’umma mai makoma ta bai daya a yankin Asiya da tekun Fasifik, wadda ke bude kofa ga sauran yankuna, da samar da ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, da inganta mu’amalar juna, gami da samun moriya tare, a wajen taro karo na 27 da aka yi ta kafar bidiyo a jiya Juma’a, tsakanin shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC.

Shawarar da kasar Sin ta bayar, da kuma sabon burin kungiyar APEC sun kama hanya daya, ana nufin mutane suna bukatar hada kai da bin ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a wannan lokaci da ake ciki. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, sakamakon illar annobar COVID-19, tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Fasifik zai gamu da koma-baya a bana, karo na farko a cikin shekaru 30 da suka gabata.

Gina al’umma mai makoma ta bai daya a yankin Asiya da tekun Fasifik zai bude sabon babi ga hadin-gwiwar kasashen yankin

Hadin-gwiwar kasashen dake yankin Asiya da tekun Fasifik na bukatar sabon shiri. A daidai wannan lokaci, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kiyaye ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban, da raya tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, al’amarin da zai kafa alkibla ga ci gaban yankin.

Kasashe membobin kungiyar APEC za su himmatu domin cimma burin da aka tsara wato burin kungiyar APEC ta shekarar 2040 ta Putrajaya. Babu tantama, kasar Sin za ta sanya sabon kuzari wajen cimma burin, ta yadda duniya za ta shaida cewa, hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Fasifik, hadin-gwiwa ce dake kawowa juna moriya da alheri.(Murtala Zhang)